Sanata Yari Ya Fadi Karfin da Tinubu zai Nuna Ya Kwarfe Atiku a Jihohi 20
- Shugaban kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce Bola Tinubu na da iko a kan jihohi sama da 20 gabanin zaben 2027
- Yari ya sanar da cewa za a kaddamar da kwamitin yakin neman zaben a ranar 14 ga Oktoba, sannan a fara yakin neman zaben a hukumance a Kaduna ranar 24 ga Oktoba
- Ya ce Atiku Abubakar da Peter Obi ba su da jihohin da za su iya cewa suna iko da su a yankunan da ba na su ba, yana mai cewa dan takara na bukatar goyon baya a ko ina
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Shugaban kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce Shugaba Bola Tinubu na da tabbacin samun nasara a jihohi sama da 20 a zaben 2027.
Yari, tsohon gwamnan Zamfara, ya bayyana hakan ne bayan ganawa da Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja, inda suka tattauna kan jadawalin yakin neman zaben da kuma ziyarar da shugaban kasar zai kai jihohi daban-daban.

Source: Twitter
Vanguard ta wallafa cewa ya kuma sanar da ranakun kaddamar da kwamitin yakin neman zaben da kuma fara yakin neman zaben a hukumance.
'Tinubu zai ci zabe a jihohi 20'
Da yake magana kan karfin ’yan takarar jam’iyyun adawa, Yari ya yi ikirarin cewa Tinubu na da goyon baya a jihohi sama da 20 na Najeriya.
Ya kuma yi ikirarin cewa dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar, da dan takarar NDC, Peter Obi, ba za su iya cewa suna da cikakken iko a kan wata jiha a wajen yankunansu ba.
Yari ya kalubalanci Atiku da ya nuna jihar da ADC ke da karfin lashe zabe a kudancin Najeriya, sannan ya tambayi ko Obi zai iya cewa yana da irin wannan karfi a jihohin Arewacin kasar.
Ya ce:
“Shin dan takarar ADC a kudancin kasar zai iya cewa yana da iko da wata jiha a kudancin Najeriya? Kuma ba na tunanin Peter Obi, wanda muka taba zama abokan aiki, zai iya cewa yana da iko da wata jiha a Arewacin Najeriya.”
Karin bayani daga Sanata Yari
Yari ya bayyana cewa samun goyon baya a wani yanki kadai ba zai wadatar wajen lashe zaben shugaban kasa ba, yana mai cewa dole ne dan takara ya samu goyon baya a Arewa da Kudu.
A cewarsa, ko da dan takara ya samu goyon bayan kaso 80 cikin 100 na masu zabe a Kudancin kasar, hakan ba zai wadatar ba idan bai samu goyon baya a Arewa ba.
Haka kuma, ya ce samun irin wannan rinjaye a Arewa ba zai wadatar ba idan dan takara bai samu goyon baya a Kudancin Najeriya ba.

Source: Facebook
Yari ya kuma yi amfani da addu’a wajen bayyana yakinin cewa Atiku da Obi ba za su iya kayar da Tinubu ba, yana mai cewa Allah ne ya ba shugaban kasar damar tallafa wa wasu daga cikin ’yan takarar adawa a baya.
Atiku ya soki Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa Atiku Abubakar ya caccaki gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan rage kudin man fetur na kwana 30.
Atiku ya ce Bola Tinubu ya kwafi tsarin da ya kawo amma ya gagara amfani da shi yadda ya kamata kamar dalibin da ba ya fahimtar karatu.
Ya tambayo Bola Tinubu me zai faru idan kwana 30 suka wuce, inda ya ce ya zama wajibi shugaban kasar ya ba 'yan Najeriya amsa.
Asali: Legit.ng


