Ana Neman Sauki, Farashin Man Fetur Ya Tashi, Lita Ta kai N1,900
- Farashin fetur a wasu diloli a Fatakwal ya tashi zuwa N1,900 kan kowace lita, duk da cewa wasu gidajen mai a Legas na sayar da shi kan farashi mai rahusa
- Kamfanonin NIPCO da wasu diloli sun kara farashin fetur, yayin da farashin dizal a wasu wurare ma ya tashi zuwa N1,900 kan kowace lita
- Hakan na zuwa ne yayin da NNPCL ya tsawaita rangwamen farashin fetur da yake bayarwa a gidajen mai a fadin Najeriya har zuwa karshen watan Oktoba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Rivers – Farashin fetur a wajen wasu diloli a Najeriya ya tashi zuwa N1,900 kan kowace lita, duk da cewa wasu gidajen mai na ci gaba da sayar da shi kan farashi mai rahusa.
Rahoton farashin man fetur na ranar Juma’a ya nuna cewa an samu karin farashi a Legas, Fatakwal, Warri da Calabar, inda diloli da dama suka kara farashin fetur da dizal.

Source: Getty Images
Vanguard ta wallafa cewa hakan na zuwa ne yayin da farashin danyen mai a kasuwannin duniya ya dan karu, tare da ci gaba da samun bambance-bambance a wajen diloli.
Diloli sun kara kudin mai
Kamfanin NIPCO ne ya jagoranci karin farashin fetur a Fatakwal, inda ya daga farashin kowace lita da N170, daga N1,730 zuwa N1,900.
Haka kuma, African Terminal, Ascon, Eterna, Gulf Treasure, Ibachem da Ibeto sun kara farashinsu daga N1,750 zuwa N1,900 kan kowace lita.
Sai dai Duport da Integrated sun kara farashin zuwa N1,806 daga N1,750, wanda ke nuna karin N56 kan kowace lita.
A Legas kuwa, Masters ya kara farashin fetur zuwa N1,350 daga N1,303, yayin da Matrix ya daga farashinsa zuwa N1,360 daga N1,330.
Sigmund da T.S.L sun kara farashin zuwa N1,350 daga N1,300, yayin da NIPCO ya daga nasa zuwa N1,350 daga N1,326.
A Calabar, Matrix ya kara farashin fetur zuwa N1,370 daga N1,315. A Warri kuma, Keonamex, Matrix, Nepal da Parker sun daga farashin zuwa N1,360 daga N1,315, yayin da Optima ya kara nasa daga N1,330 zuwa N1,360.

Kara karanta wannan
Bayan rage farashi, Gwamnatin Tinubu ta yi bayani kan yiwuwar dawo da tallafin fetur kafin 2027

Source: Getty Images
Farashin fetur ya bambanta
A bangaren gidajen mai, NNPCL na sayar da fetur kan N1,360 a kowace lita a gidajen marta da ke Legas da kewaye.
MRS na sayar da fetur kan N1,338, yayin da 11 Plc ke sayar da shi kan N1,338.80.
A gefe guda, dillalan mai masu zaman kansu na sayar da fetur kan farashin da ya kama daga N1,368 zuwa N1,400, gwargwadon wurin da suke.
NNPCL ya rage N66
A wani labarin, kun ji cewa NNPCL ya sanar da tsawaita rangwamen farashin fetur da take bayarwa a gidajen mai na fadin Najeriya.
Kamfanin ya ce ya fara bayar da rangwamen ne a ranar 1 ga Oktoba, domin bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kan Najeriya.
Tsawaita rangwamen na daga cikin matakan rage tasirin tsadar danyen mai a kasuwannin duniya ga iyalai, ’yan kasuwa a fadin kasar nan.
Asali: Legit.ng
