NNPCL Ya Cigaba da Garabasar Rage Kudin Fetur ga 'Yan Najeriya
- Kamfanin NNPCL ya ƙara tsawon mako guda a shirin rangwamen N66 a kowace litar fetur da dizil domin bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun 'yancin kai
- Masu sayen fetur ta hanyar manhajar NNPC za su ci gaba da cin moriyar wannan rangwame har zuwa ranar 14 ga watan Oktoban 2026
- Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta sanar da shirin rage farashin fetur na tsawon kwana 30 domin rage radadin rayuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Kamfanin harkar mai na NNPCL ya ƙara tsawon mako guda kan shirin rangwamen farashin fetur na bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun 'yancin kai wanda aka fara a ranar 1 ga watan Oktoban 2026.
A karkashin wannan shiri, abokan ciniki da ke sayen man fetur ta hanyar amfani da manhajar NNPC suna samun sauƙin N66 a kowace lita guda.

Source: Getty Images
Legit ta gano cewa kamfanin NNPCL ya fitar da sanarwar kara wa'adin ne a wani sako da ya wallafa a Facebook a ranar 9 ga Oktoban 2026.
NNPCL na garabasar mai
Sakamakon cika wa’adin sati guda na farko, kamfanin NNPCL ya yanke shawarar tsawanta shirin garabasar man da ƙarin mako guda, tare da haɗawa da man dizil irin na AGO.
NNPCL ya sanar da cewa cewa:
"Ƙarin mako guda. An ƙara tsawon shirin rangwamen N66 kan man fetur da mako guda, kuma yanzu an haɗa da mai nau'in dizil na AGO."
Ya kara da cewa:
"Za ku iya ziyartar duk wani gidan mai na NNPC domin cin moriyar shirin har zuwa ranar 14 ga Oktoba, 2026."
Matakan gwamnati na rage radadi
Wannan tallafi na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta sanar da tsarin rage farashin fetur a gidajen man NNPCL na tsawon kwana 30 domin sauƙaƙa matsin rayuwa ga 'yan ƙasa.
Ministan Kuɗi da Tattalin Arziki, Taiwo Oyedele, ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin wani taron manema labarai a Abuja, inda ya ce wannan mataki zai fifita masu sana'ar sufurin jama'a waɗanda tsadar fetur ta fi shafa.

Source: Getty Images
Gwamnatin ta nuna cewa ana yin hakan ne domin daidaita farashin kayayyaki da sauƙaƙa kuɗin sufuri ga al'umma baki ɗaya.
NLC ta nemi rage kudin mai
A wani labarin, mun ruwaito cewa ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta ba gwamnatin tarayya wa'adin sati biyu domin rage farashin man fetur da sake gudanar da tattaunawa kan mafi ƙancin albashi na ƙasa.
Sanarwar wadda Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya sanya wa hannu bayan taron haɗin gwiwa na NEC da CWC a birnin Abuja, ta nuna cewa wa'adin zai fara ne daga ranar Juma'a, 9 ga watan Oktoba, 2026.
NLC ta buƙaci mambobinta da ƙungiyoyi masu zaman kansu da su kasance a shirye domin ɗaukar matakan sakamako idan har gwamnati ta ƙasa biyan buƙatun ma'aikatan bayan cika wa'adin.
Asali: Legit.ng

