'Yan Kwadago za Su Fara Sabon Rikici da Tinubu kan Rage Farashin Fetur
- Kungiyar kwadago ta NLC ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin mako biyu ta rage farashin man fetur tare da fara tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashi
- NLC ta ce wa’adin zai fara ne daga Juma’a, 9 ga Oktoba, 2026, tare da gargadin daukar matakan da suka dace idan gwamnati ta gaza cika bukatunta
- Kungiyar ta kuma bukaci gwamnati ta aiwatar da yarjejeniyoyin da ta cimma da ma’aikatan lafiya da sauran ma’aikatan gwamnati
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin kwana 14 ta dauki matakan rage farashin man fetur da fara tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashi.
NLC ta bayyana hakan ne a cikin sanarwar hadin gwiwa da ta fitar bayan wani taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) da kwamitin ayyuka (CWC), wanda aka gudanar a Labour House da ke Abuja.

Kara karanta wannan
Wata mata ta fito fili ta bayyana cewa tana taimaka wa yan ta'adda a Arewacin Najeriya

Source: Facebook
Vanguard ta wallafa cewa shugaban NLC, Joe Ajaero, ya ce wa’adin zai fara daga Juma’a, 9 ga Oktoba, 2026. Ya kuma bukaci rassan kungiyar da abokan tafiyarta su kasance cikin shirin daukar mataki idan gwamnati ta gaza biyan bukatunta.
NLC ta nemi karin albashi
Kungiyar ta ce hauhawar farashin kayayyaki da faduwar darajar Naira sun rage darajar albashin ma’aikata, har ya zama ba sa iya biyan muhimman bukatun rayuwa.
A cewar NLC, ma’aikata na fuskantar matsala wajen biyan kudin abinci, muhalli, kiwon lafiya, sufuri da ilimi da albashin da suke karba a yanzu.
Saboda haka, kungiyar ta bukaci gwamnatin tarayya ta fara tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashi kafin karshen watan Oktoba, tana mai cewa ba za ta amince da jinkiri ba.
An bukaci a rage farashin fetur
Punch ta wallafa cewa NLC ta kuma bukaci gwamnatin tarayya ta yi aiki da hukumomin da abin ya shafa domin rage farashin man fetur a fadin Najeriya.
Kungiyar ta ce tsadar man fetur ta kara kudin sufuri, abinci da sauran kayayyakin masarufi, lamarin da ya kara tsananta halin kuncin rayuwa ga ma’aikata da sauran ‘yan kasa.
Ta bukaci gwamnati ta sauya manufofin da ta ce sun janyo karin farashin man fetur ba tare da tsari ba, tana mai cewa hakan na amfanar wasu ‘yan kasuwa yayin da jama’a ke kara shiga talauci.

Source: Facebook
Batun yarjejeniyoyin ma’aikata
Daga cikin bukatun da kungiyar ta gabatar akwai aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma da Kungiyar Hadin Gwiwar Kungiyoyin Ma’aikatan Lafiya (JOHESU) a ranar 5 ga Fabrairu, 2026.
Haka kuma, ta bukaci gwamnati ta aiwatar da bukatun Majalisar Tattaunawar Ma’aikatan Gwamnati (JPSNC).
NLC ta yi gargadin cewa idan gwamnati ta gaza cika wadannan bukatu cikin wa’adin da ta bayar, za ta dauki matakan da hukumomin shugabancinta za su amince da su.
Kungiyar ta bukaci ma’aikata da abokan tafiyarta su kasance cikin shiri, tana mai jaddada cewa za ta ci gaba da adawa da duk wani abu da take ganin yana zaluntar ma’aikata da sauran jama’a.
Tinubu zai rage kudin mai
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta sanar da shirin rage farashin man fetur a gidajen mai na Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL) na tsawon kwana 30.
Ministan Kudi kuma mai kula da tattalin arziki, Taiwo Oyedele, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis.
Oyedele ya ce shirin zai fi mayar da hankali kan masu gudanar da motocin sufuri, wadanda tsadar man fetur ta fi shafa a Najeriya.
Asali: Legit.ng

