Da Gaske Gwamnatin Tarayya Ta Dawo da Tallafin Mai a Fakaice bayan Rage Farashi?

Da Gaske Gwamnatin Tarayya Ta Dawo da Tallafin Mai a Fakaice bayan Rage Farashi?

  • Kamfanin NNPCL ya ce ya fara rangwamen Naira 66 kan kowace litar fetur tun ranar 1 ga Oktoba, domin bikin cikar Najeriya shekaru 66
  • Kamfanin ya bayyana cewa rangwamen zai ci gaba har zuwa ranar 31 ga Oktoba, 2026, kuma manufarsa ita ce rage wa ’yan Najeriya radadin tsadar man fetur
  • NNPCL ya jaddada cewa rangwamen ba yana nufin dawo da tallafin man fetur ba, kuma bai sauya tsarin farashin da kasuwa ke kayyadewa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Kamfanin Mai na Najeriya (NNPCL) ya yi magana bayan gwamnatin tarayya ta sanar da rage farashin mai.

NNPCL ya ce kwastomominsa sun dade suna cin moriyar rangwamen Naira 66 kan kowace litar fetur kafin sanarwar gwamnatin tarayya.

NNPCL ya magantu kan rangwamen man fetur a Najeriya
Wani ma'aikacin gidan mai yana zuba fetur a mota da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga, Contributor.
Source: Getty Images

Hakan na cikin wata sanarwa, babban jami’in hulɗa da jama’a na kamfanin NNPCL, Andy Odeh da ya wallafa a X.

Kara karanta wannan

NNPCL ya cigaba da garabasar rage kudin fetur ga 'yan Najeriya

Odeh ya ce sun fara rangwamen Naira 66 ne ranar 1 ga Oktobar shekarar 2026 bayan cikar kasar shekaru 66.

Ya kuma jaddada cewa matakin ba yana nufin dawo da tallafin man fetur ba kamar yadda wasu ke yaɗawa.

Ya bayyana cewa an fara rangwamen ne domin bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai, kuma zai ci gaba har zuwa ranar 31 ga Oktoba.

Sanarwar ta ce:

“Tun kafin sanarwar, kamfanin NNPC Limited ya fara rangwamen farashin fetur a ranar 1 ga Oktoba, 2026, domin bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai."

Abin da NNPCL ya ce kan rangwamen

NNPCL ya kuma jaddada cewa wannan shiri ya dace da matakan gwamnatin tarayya na samar da agajin da zai taimaka wa ’yan Najeriya a lokacin da ake fuskantar rashin tabbas a kasuwannin duniya.

Kamfanin ya ce matakin zai taimaka wajen rage wa jama’a radadin hauhawar farashin kayayyaki da mai ba tare da dawo da tallafin man fetur ba.

Kara karanta wannan

Bayan rage farashi, Gwamnatin Tinubu ta yi bayani kan yiwuwar dawo da tallafin fetur kafin 2027

“Wannan shiri ya shafi gidajen sayar da mai na NNPC Retail ne kawai, kuma ba ya nufin cewa an kafa farashi guda ɗaya na fetur a duk faɗin ƙasar nan.
“Haka kuma, rangwamen bai sauya tsarin kayyade farashin man fetur bisa yanayin kasuwa ba.”

Kamfanin ya ƙara da cewa yana aiki tare da gwamnatin tarayya da sauran masu ruwa da tsaki domin rage tasirin tashin farashin fetur ga iyalai, ’yan kasuwa da tattalin arzikin ƙasa baki ɗaya.

“Mun fahimci cewa hauhawar farashin fetur na shafar rayuwar yau da kullum, tun daga kuɗin sufuri zuwa kuɗin gudanar da harkokin kasuwanci.
“Mun fahimci matsin da iyalai da masu neman abin dogaro da kai ke fuskanta, kuma an tsara wannan rangwame ne domin ba kwastomomi tallafin kai tsaye a wannan mawuyacin lokaci.
“Muna godiya ga ’yan Najeriya bisa ci gaba da amfani da kayayyakinmu da goyon bayan da suke ba mu. Muna kuma ci gaba da jajircewa wajen samar da sahihan bayanai game da kayayyakinmu, farashinsu da shirye-shiryen tallafa wa kwastomomi.”

- Cewar NNPCL

Sanarwar ta ƙara da cewa kamfanin NNPC Limited zai ci gaba da tabbatar da samar da fetur yadda ya kamata tare da haɗin gwiwa da gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki domin rage wa ’yan Najeriya nauyin tsadar rayuwa.

Kara karanta wannan

Sauki ya zo: NNPCL ya kawo tsarin sayen fetur da arha a fadin Najeriya

NNPCL ya kara wa'adin rage farashin mai

A wani labarin, an ji cewa Kamfanin NNPCL ya ƙara tsawon mako guda a shirin rangwamen N66 a kowace litar fetur da dizil domin bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun 'yancin kai.

Masu sayen fetur ta hanyar manhajar NNPC za su ci gaba da cin moriyar wannan rangwame har zuwa ranar 14 ga watan Oktoban 2026.

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta sanar da shirin rage farashin fetur na tsawon kwana 30 domin rage radadin rayuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.