Akwai Yiwuwar Amaechi Ya Bar Gwamnatin Atiku idan Suka Hau Mulki
- Rotimi Amaechi ya ce zai iya yin murabus daga muƙamin mataimakin shugaban ƙasa a gwamnatin Atiku Abubakar
- Ya yi hasashen cewa idan ADC ta lashe zaɓen 2027, ’yan Najeriya za su yaba wa Atiku tare da kallonsa a matsayin gwarzo cikin shekarar farko
- Amaechi ya buƙaci masu zaɓe su tantance ayyukan da ya gudanar a matsayin gwamna, minista da kakakin majalisar dokokin jihar Rivers kafin su yanke shawara.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa zai iya yin murabus daga gwamnatin Atiku Abubakar idan suka samu nasara.
Amaechi ya ce a shirye yake ya yi murabus idan gwamnatin Atiku Abubakar ta gaza gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.

Source: Twitter
Amaechi ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar News Central TV, inda ya yi magana kan shirin ADC da irin tarihin ayyukan da yake son ’yan Najeriya su tantance kafin zaɓen 2027.

Kara karanta wannan
"Ku ce ni da Kwankwaso mun gaza"; Peter Obi ya dauki muhimmin alkawari ga 'yan Najeriya
Tsohon ministan sufuri ya ce Atiku ya san halayensa, yana mai hasashen cewa idan ADC ta samu nasara, ’yan Najeriya za su yaba wa tsohon mataimakin shugaban ƙasar cikin shekarar farko ta mulkinsa.
Amaechi ya ce zai iya barin gwamnati
Amaechi ya bayyana cewa ba zai ci gaba da zama a gwamnati ba idan ya fahimci cewa ba sa gudanar da ayyukan da ya kamata.
“Na tabbata ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC ya san halayena, domin idan ba mu gudanar da ayyukanmu yadda ya kamata ba, akwai yiwuwar na bar gwamnati.” In ji shi.
Lokacin da aka tambaye shi ko yana nufin zai iya yin murabus daga muƙamin mataimakin shugaban ƙasa idan gwamnatin Atiku da shi ta gaza aiki, Amaechi ya amsa kai tsaye.
"Eh, ba wasa nake yi ba. Amma bisa yadda lamarin yake da kuma yadda na san Atiku, a shekararmu ta farko a mulki, za a yaba masa a matsayin gwarzo.” In ji shi.
Ya yi hasashen Atiku zai zama gwarzo
Tsohon gwamnan jihar Rivers ya kuma bayyana cewa ’yan Najeriya za su yi nadamar rashin zaɓen Atiku tun da wuri idan ya zama shugaban ƙasa.
“Za a yaba wa Atiku a matsayin gwarzo. ’Yan Najeriya za su yi nadamar rashin zaɓensa tun kafin wannan lokaci.” In ji shi.
Da aka tambaye shi ko zai cika alƙawuran da yake yi wa jama’a, Amaechi ya ƙalubalanci duk wanda ya ce ya taɓa yi masa alƙawari amma ya ƙi cikawa da ya fito ya bayyana hakan.
Ya kuma buƙaci ’yan Najeriya su yi la’akari da tarihin ayyukansa a muƙaman gwamnati daban-daban da ya riƙe a baya.
A cewarsa, ya kamata a tantance shi bisa ayyukan da ya gudanar lokacin da yake gwamnan Rivers, ministan sufuri da kuma kakakin majalisar dokokin jihar.

Source: Facebook
Shettima ya ragargaji Amaechi
A wani labarin kuma, kun ji cewa Kashim Shettima, ya soki tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, kan zargin cewa marigayi Muhammadu Buhari ya yi masa alƙawarin tikitin takarar shugaban ƙasa na APC a 2023, amma daga baya ya karya alƙawarin.
Mataimakin shugaban kasar ya bayyana zargin a matsayin magana marar dacewa da rashin girmamawa ga tarihin marigayi Muhammadu Buhari.
Asali: Legit.ng
