Kakar Miliyoyin Matasa Ta Yanke Saƙa, An Fadada Shirin Tallafin Rage Talauci a Najeriya
- Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da wani shiri na rage talauci da ke da burin taimaka wa ’yan Najeriya miliyan biyar cikin shekaru huɗu masu zuwa
- An horar da matasa 700 a jihar Oyo kan fasahar AI, zane-zanen kwamfuta da sana’o’in dogaro da kai
- Waɗanda suka kammala horon sun samu kwamfutoci, kayan aikin kwalliya, injinan ɗinki da allunan kwamfuta domin taimaka musu su fara sana’o’i
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Oyo, Nigeria - Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da faɗaɗa shirin yaki da talauci da ke da burin fitar da ’yan Najeriya miliyan biyar daga talauci cikin shekaru huɗu masu zuwa.
Gwamnatin ta horar da matasa 700 a jihar Oyo kan fasahar (AI), zane-zanen kwamfuta da sana’o’in dogaro da kai.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa ana gudanar da shirin ne ta ofishin Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Ilimin Fasaha, Sana’o’i da Kasuwanci (OSSAP-TVEE).

Kara karanta wannan
Ya mutane za su samu fetur mai araha a garuruwan da babu gidan man NNPC? An aika sako ga Tinubu
Abin da shirin rage talauci ya kunsa
Shirin na da nufin magance rashin aikin yi, rage gibin ƙwarewa da kuma samar wa waɗanda za su amfana da kayan aikin da za su taimaka musu kafa sana’o’i da shiga harkokin tattalin arzikin zamani.
Shirin horarwar da aka gudanar a jihar Oyo daga ranar 28 ga Satumba zuwa 9 ga Oktoba, 2026, ya ƙare a ranar Juma’a da bikin yaye mahalarta a dakin taron Jami’ar Ibadan.
A wajen bikin, an ba mahalarta kayan aiki da na’urori domin taimaka musu sauya ƙwarewar da suka samu zuwa sana’o’in da za su samar musu da kuɗin shiga.
Dalilin fadada shirin a Najeriya
Da take jawabi a wajen bikin, Babbar Mataimakiya ta Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Ilimin Fasaha, Sana’o’i da Kasuwanci, Dakta Abiola Arogundade, ta ce shirin ya nuna jajircewar Shugaba Bola Tinubu wajen yaƙi da talauci.
“Abin da muke son yi, kuma abin da Shugaban Ƙasa yake son yi, shi ne fitar da mutane da dama daga talauci gwargwadon iko.

Kara karanta wannan
An ga tashin hankali da 'yan ta'adda suka hallaka sojoji da dan kasar waje a Kebbi
“Shugaban Ƙasa ya yi imanin cewa matasanmu ba tallafi kawai suke buƙata ba. Suna buƙatar dama, suna buƙatar ƙwarewa, suna buƙatar kayan aikin da za su taimaka musu yin gogayya da wasu da kuma gina hanyoyin samun abin dogaro,” in ji Arogundade.
Ta ce an tsara shirin ne domin bai wa matasan Najeriya ƙwarewar aiki da kayan aikin da za su taimaka musu mayar da ilimin da suka samu zuwa sana’o’in da za su iya samar musu da kuɗin shiga, cewar rahoton Tribune Nigeria.

Source: Facebook
Kayayyakin da aka raba wa waɗanda suka amfana sun haɗa da kwamfutocin tafi-da-gidanka, kayan aikin kwalliya, injinan ɗinki da allunan kwamfuta, gwargwadon irin horon da kowane mai cin gajiyar dhirin ya samu da tallafin da aka tanadar masa.
Gwamnati ta fara daukar bayanan matasa
Kun ji cewa Gwamnatin tarayya ta bukaci ’yan Najeriya matasa masu shekaru tsakanin 15 zuwa 35 su yi rajista da shirin NYDB.
Ta ce rijistar za ta shafi matasa da ke bangaren aiki na hukuma da wadanda ke gudanar da sana’o’in kansu, ciki har da masu aikin gona, wasanni, masana’antun kirkire-kirkire da fasaha.
Asali: Legit.ng