Najeriya Ta Yi Rashi da 'Yan Bindiga Suka Hallaka Jami'in Tsaro a Plateau

Najeriya Ta Yi Rashi da 'Yan Bindiga Suka Hallaka Jami'in Tsaro a Plateau

  • Wasu ’yan bindiga sun kashe wani jami’in tsaro a kusa da Kwi, tsakanin ƙananan hukumomin Riyom da Barkin Ladi a jihar Plateau
  • Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 7:00 na yammacin Alhamis, lokacin da jami’in ke kan babur zuwa wurin aikinsa a yankin Chit na Heipang
  • Kakakin ƙungiyar Berom Youth Moulders-Association ya yi Allah-wadai da kisan, yana mai kira da a ɗauki matakan gaggawa domin inganta tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Plateau - Wasu ’yan bindiga sun kashe wani jami’in tsaro yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa wurin aikinsa a kan hanyar Kwi-Beco da ke jihar Plateau.

Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:00 na yammacin ranar Alhamis, 8 ga watan Oktoban 2026 a yankin Kwi, tsakanin ƙananan hukumomin Riyom da Barkin Ladi na jihar.

Kara karanta wannan

To fa: Gwamnatin tarayya ta yi gargadi kan sababbin hanyoyin da 'yan ta'adda suka bullo da su

An kashe jami'in tsaro a Plateau
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Disu Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

An kashe jami’in a kan hanyar zuwa aiki

Rahotan jaridar Vanguard ya nuna cewa jami’in tsaron na kan babur ne zuwa wurin aikinsa da ke yankin Chit, a Heipang, lokacin da maharan suka kai masa hari suka kashe shi.

Majiyoyin sun ƙara da cewa maharan sun yi awon gaba da babur ɗin jami’in bayan sun kashe shi.

Ƙungiyar Berom ta yi Allah-wadai da kisan

Kakakin ƙungiyar Berom Youth Moulders-Association (BYM), Rwang Tengwong, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana kisan a matsayin abin tayar da hankali.

Tengwong ya ce kashe jami’in tsaro ya haifar da babbar damuwa kan tsaron fararen hula da ke zaune a al’ummomin yankin.

Ya bayyana cewa abin damuwa ne yadda jami’an tsaro da aka tura domin kare al’umma su ma ke fuskantar hare-hare.

An yi kira da a ƙarfafa tsaro

Kakakin ƙungiyar ya yi Allah-wadai da kisan, tare da kira ga hukumomin da abin ya shafa da su ɗauki matakan gaggawa domin magance matsalolin tsaro da ke addabar al’ummomin yankin.

Kara karanta wannan

An ga tashin hankali da 'yan ta'adda suka hallaka sojoji da dan kasar waje a Kebbi

Sai dai har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, ba a samu nasarar tuntubar jami’an tsaro domin samun tabbaci a hukumance kan lamarin ba.

Karanta karin wasu labaran kan 'yan bindiga

An kashe jami'in tsaro a Plateau
Taswirar jihar Plateau, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

An kashe jagoran 'yan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa an kashe wani fitaccen shugaban dabar ’yan bindiga, Kachalla Mu’azu, da wasu manyan yaransa shida a jihar Zamfara da ke Arewa maso Yamma.

Dan ta'addan, wanda ya addabi al'umma ya yi bankwana da duniya ne a wani artabu tsakanin ƙungiyoyin ’yan bindiga masu hamayya da juna a jihar Zamfara.

Kachalla Mu’azu da mutanensa suna dawowa ne daga Kasuwar Yankara lokacin da mambobin wata dabar ’yan bindiga suka kai musu harin kwanton bauna a kan hanyar da suke bi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng