Tsaro Ko Tazarcen Tinubu: Matawalle Ya Bayyana Babban Burinsa a 2027

Tsaro Ko Tazarcen Tinubu: Matawalle Ya Bayyana Babban Burinsa a 2027

  • Bello Matawalle ya bayyana cewa babban burinsa bayan gudanar da aikinsa a Ma’aikatar Tsaro shi ne taimakawa Tinubu ya sake lashe zaɓen 2027
  • Ministan ya buƙaci mambobin APC a Zamfara su haɗa kai tare da ƙara himma wajen yaɗa manufofin jam’iyyar da neman nasararta
  • Matawalle ya yi alƙawarin tura ƙarin jami’an tsaro kan manyan hanyoyin Zamfara domin kare matafiya daga hare-haren ’yan bindiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Zamfara - Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya bayyana cewa babban burinsa shi ne ganin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Matawalle ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a gidansa da ke Gusau, babban birnin Jihar Zamfara a ranar Alhamis, 12 ga watan Nuwamban 2026.

Kara karanta wannan

Jigo a ADC ya gano abin da Tinubu ke fargaba kan zaben 2027

Matawalle ya yi magana kan Tinubu
Bello Matawalle tare da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bello Matawalle
Source: Twitter

Taron ya gudana ne gabanin ziyarar da ake sa ran uwargidan shugaban ƙasa, Sanata Remi Tinubu, za ta kai jihar, cewar rahoton tashar Channels tv.

Ministan ya buƙaci mambobin APC su haɗa kai tare da ƙara himma wajen wayar da kan jama’a domin ganin Tinubu ya sake lashe zaɓe, da kuma samun nasarar sauran ’yan takarar jam’iyyar a jihar.

Matawalle ya bayyana burinsa kan zaɓen 2027

Matawalle ya yaba wa ƙoƙarin Tinubu wajen magance matsalar tsaro, bunƙasa ababen more rayuwa da kuma ƙarfafa haɗin kan siyasa a ƙasar nan.

Ya bayyana aniyarsa ta ganin shugaban ƙasar ya kammala wa’adinsa na shekaru takwas a kan mulki.

Ministan ya ce bayan ya sauke nauyin da ke kansa a matsayin Ministan Tsaro, musamman wajen yaƙi da matsalar rashin tsaro, babban abin da zai mayar da hankali a kai shi ne taimaka wa Tinubu ya sake lashe zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

An buga kugen siyasa; Pantami ya aika da zazzafan sako ga 'yan takarar gwamnan Gombe

Ya kuma yi watsi da abin da ya kira tsokana da farfaganda daga wasu mutane da ke ƙoƙarin ɓata masa suna.

Matawalle ya ce babban abin da ya dame shi shi ne tabbatar da haɗin kai tsakanin mambobin APC a Zamfara da kuma samun nasarar jam’iyyar a dukkan matakan zaɓe.

Ya yi magana kan lafiyar Tinubu

Ministan ya kuma yi watsi da zarge-zarge da farfagandar da ake yaɗawa game da lafiyar Shugaba Tinubu.

Ya dage cewa shugaban ƙasar yana cikin ƙoshin lafiya kuma yana da ƙarfin ci gaba da jagorantar Najeriya.

Matawalle ya je Zamfara
Bello Matawalle na jawabi ga jama'a a Zamfara Hoto: Ahmad Dan-Wudil
Source: Facebook

Za a ƙara jami’an tsaro a Zamfara

Dangane da matsalar tsaro, Matawalle ya tabbatar wa mazauna Zamfara cewa gwamnatin tarayya za ta tura ƙarin jami’an tsaro zuwa manyan hanyoyin jihar domin kare matafiya daga hare-haren ’yan bindiga.

Ya ambaci hanyar Talata Mafara-Gusau-Sokoto a matsayin ɗaya daga cikin wuraren da za a ƙara tsaro.

Haka kuma, ya ce za a ƙara jami’an tsaro a hanyoyin Gummi-Anka-Bukkuyum da kuma hanyar shiga Tsafe.

Matawalle ya ba 'yan majalisun APC motoci

A wani labarin kuma, kun ji cewa karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya bai wa wasu ’yan majalisar dokokin Zamfara takwas motoci bayan sun koma jam’iyyar APC.

’Yan majalisar sun koma APC mai mulki ne a wani mataki na ƙarfafa jam’iyyar gabanin babban zaɓen shekarar 2027 mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng