'Yan Bindiga Sun Tafka Barna bayan Kai Kazamin Hari a Kebbi

'Yan Bindiga Sun Tafka Barna bayan Kai Kazamin Hari a Kebbi

  • ’Yan bindiga sun kai hari Kasabo da ke Saminaka, ƙaramar hukumar Yauri ta Kebbi, inda suka kashe mutane uku kafin su koma maboyarsu
  • Mazauna yankin sun tsere ta cikin daji yayin harin, bayan ’yan bindigar sun shigo cikin garin da dimbin yawa
  • Gwamna Nasir Idris ya bayar da N116m ga iyalan waɗanda aka kashe da al’ummar yankin, tare da alkawarin ƙara haɗin gwiwa da jami’an tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kebbi - ’Yan bindiga sun kai hari a Kasabo, wata al’umma da ke Saminaka, ƙaramar hukumar Yauri ta jihar Kebbi, inda suka kashe mutane uku.

Rahotanni sun ce ’yan bindigan dauke da makamai sun kai harin ne da sanyin safiyar ranar Litinin, 5 ga watan Oktoban 2026 na wannan mako.

Yan bindiga sun kashe mutane a Kebbi
Taswirar jihar Kebbi, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Mazauna garin sun tsere ta cikin daji

Kara karanta wannan

Kwamishinan 'yan sandan Kano ya yaba wa Sarki Aminu Ado kan muhimmin abin da ya yi

Wani mazaunin yankin, Aminu Salisu, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa maharan sun shigo garin cikin adadi mai yawa.

Ya bayyana cewa mazauna garin da dama sun yi nasarar tserewa ta cikin daji domin kuɓuta daga harin.

“Amma sun yi nasarar kashe mutane uku kafin su koma maboyarsu,” in ji Aminu Salisu.

Ba a bayyana ƙarin bayanai kan mutanen da aka kashe ko kuma ko an samu wasu raunuka a harin ba.

Gwamnan Kebbi ya ziyarci garin

A yayin ziyarar ta’aziyya da ya kai wa al’ummar yankin ranar Talata, 6 ga watan Oktoban 2026, Gwamnan Kebbi, Nasir Idris, ya bayyana harin a matsayin mummunan lamari da kuma abin da ba za a amince da shi ba.

Gwamnan ya ce kisan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, wani mummunan tashin hankali ne da ya shafi rayukan al’umma.

Ya bayar da tallafin N116m ga iyalan waɗanda aka kashe da kuma al’ummar yankin domin rage musu raɗaɗin da lamarin ya jawo.

Gwamna ya yi alkawarin ƙarfafa tsaro

Kara karanta wannan

Ana cikin jimamin hatsarin jirgi, an shiga sansanin sojojin Najeriya an kashe sama da 10

Gwamna Idris ya tabbatar wa al’ummar cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ƙarfafa haɗin gwiwa da hukumomin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Ya kuma ce gwamnatin za ta ɗauki dukkan matakan da suka dace domin tabbatar da tsaron al’ummar jihar da hana sake aukuwar irin wannan hari.

Dan Masani ya bayyana damuwa

Da yake mayar da martani, Dan Masani na Saminaka, Alhaji Mohammed Bashir, ya bayyana kisan mutanen uku a matsayin babban rashi ga al’ummar yankin.

Ya ce mutanen da aka rasa sun kasance ɓangare na al’umma, lamarin da ya jefa jama’ar yankin cikin jimami da alhini.

'Yan bindiga sun yi barna a Kebbi
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris na jawabi Hoto: Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu
Source: Facebook

'Yan bindiga sun sace matafiya

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sun tare babbar hanyar Gusau zuwa Sokoto a Jihar Zamfara, inda suka sace aƙalla matafiya 30 a sabon harin da aka kai kan hanyar.

Wani ganau, wanda ke sana’ar Achaba kuma ya nemi a ɓoye sunansa, ya ce an sace dukkan fasinjojin da ke cikin motoci ukun da 'yan bindigan suka tare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng