Rikici Ya Kara Kamari, An Kashe Tsohon Shugaban Kungiyar Matasa Ta BYM a Arewa
- ’Yan bindiga sun kashe Rwas Paul Danladi, shugaban matasa kuma tsohon shugaban kungiyar matasa Berom (BYM) a Filato
- An kai hare-hare daban-daban a Barkin Ladi da wasu sassan Jihar Filato, inda aka jikkata wasu mutane biyu
- Kungiyar BYM ta yi kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da bincike, tare fa kama waɗanda suka aikata kisan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Pleateau, Nigeria - ’Yan bindiga sun kashe wani shugaban matasa kuma tsohon shugaban Berom Youth Moulders-Association (BYM) na Gashish a jihar Filato, Rwas Paul Danladi.
Bayan kashe jagoran matasan, yan ta'addan sun kuma jikkata wasu mutane biyu a hare-hare daban-daban a karamar hukumar Barkin Ladi da wasu sassan Jihar Filato.

Source: Original
Vanguard ta ruwaito cewa an kai wa Danladi hari da misalin ƙarfe 6 na yammacin ranar Laraba a kusa da ƙauyen Rantis da ke kan hanyar Gashish zuwa Barkin Ladi, yayin da yake komawa gida a kan babur.

Kara karanta wannan
Dubu ta cika: An kama wanda ya kashe malamin addinin Musulunci a Arewacin Najeriya
Kungiyar BYM ta tabbatar da kisan
Kungiyar matassn Berom (BYM) ta tabbatar da kisan a cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na ƙasa, Rwang Tengwong, ya sanya wa hannu, wadda aka rabawa manema labarai a Jos yau Alhamis.
A cewar ƙungiyar:
"An kai wa Rwas Paul Danladi hari ne a yammacin Laraba a kusa da ƙauyen Rantis yayin da yake komawa Barkin Ladi a kan babur.”
BYM ta yi Allah-wadai da kisan, inda ta bayyana Danladi a matsayin jagoran al’umma mai daraja, tare da mika ta’aziyyarta ga iyalansa, abokansa da al’ummar Gashish baki ɗaya.
Mahara sun jikkata mutane
Ƙungiyar ta ce an kuma samu wasu hare-hare a sassan al’ummomin Berom ranar Laraba, inda aka jikkata mutane biyu, kamar yadda Premium Times ta rahoto.
A cewar BYM, an jikkata wani mutum sosai bayan an kai masa hari a kusa da Gwom-Ajang da ke Foron, kuma an garzaya da shi Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos domin yi masa magani.
Ƙungiyar ta ƙara da cewa wani mai suna, Mafeng Samuel Lamba ya samu rauni a kan hanyar Sho, sannan aka kai shi asibiti.
Kira ga hukumomin tsaro
Ƙungiyar ta yi kira ga gwamnatin Jihar Filato, Rundunar ’Yan Sandan Najeriya, Rundunar Sojin Najeriya, Hukumar Tsaro ta Ƙasa (DSS) da sauran hukumomin tsaro da abin ya shafa da su gaggauta gudanar da bincike kan kisan.
Ta kuma bukaci kama waɗanda ke da hannu tare da ƙara sa ido a kan hanyoyi da al’ummomin da ke cikin haɗari a Barkin Ladi, Jos South, Riyom da sauran yankunan da abin ya shafa.

Source: Twitter
BYM ta kuma buƙaci hukumomin tsaro da su ƙara tattara bayanan sirri tare da ɗaukar matakan kariya tun da wuri domin hana sake kai hare-hare da kuma kare mazauna yankunan.
Ankashe masu hakar ma'adanai
Kun ji cewa akalla masu haƙar ma’adinai biyar sun mutu yayin da wasu ’yan bindiga suka rutsa su a ramin hakar ma'adanai a jihar Filato.
Rahotanni sun nuna cewa wasu mutum biyu sun samu raunuka a harin da aka kai yankin karamar hukumar Barkin Ladi.
Asali: Legit.ng
