Man Ugwueje: Sojan da Ya Mutu a Hadarin Jirgin Sama Kwana 16 da Yin Aure
- Ahamefule Aham Man-Ugwueje yana cikin sojojin da suka mutu a hadarin jirgin saman NAF da aka yi a Ondo
- Gwamnan Abia ya fitar da ta’aziyya ga ‘yanuwa da daukacin mutanen da rashin matashin jami'in sojan ya shafa
- Squadron Leader Man-Ugwueje ya mutu ne makonni biyu da daura masa aure da wata sahibarsa soji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abia - Gwamnan jihar Abia, Alex Otti, ya aika ta’aziyyar rasuwar Squadron Leader Ahamefule Aham Man-Ugwueje.
Squadron Leader Ahamefule Aham Man-Ugwueje haifaffen Abia ne wanda yana cikin sojojin da jirgin sama ya kashe.

Source: Facebook
Gwamnan Abia ya yi ta'aziyyar Aham Man-Ugwueje
Premium Times ta ce Gwamna Alex Otti ya fitar da ta’aziyyar rasuwar daya daga cikin sojojin da suka mutu a hadarin jirgi.
Marigayi Ahamefule Aham Man-Ugwueje ya fito ne daga karamar hukumar Umuahia, babban birnin jihar Abia a Najeriya.
Da shi jirgin sojojin sama na ATR-42 mai lamba NAF 931 ya kife ya kashe mutane har 25 a kan hanyar Legas daga Benin.
Alex Otti ya aiko da ta’aziyya ta hannun Mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Mista Ferdinand Ekeoma a jiya.
Ferdinand Ekeoma ya bayyana mutuwar a matsayin mai ciwo da bakin ciki, ya ce ya kawo mummunan takaici da bacin rai.
Bakin cikin ya shafi ‘yanuwa, abokan arziki, masoya, sojojin sama da Gwamnati da mutanen Najeriya.
Gwamnan ya ce:
“Wannan hatsari abin takaici ne matuƙa, domin ya jefa iyalan waɗanda abin ya shafa, abokansu da masoyansu, Rundunar Sojin Sama ta Najeriya da ma ƙasa baki ɗaya cikin tsananin baƙin ciki da alhini.”
Soja ya mutu makonni 2 da yin aure
Gwamnan ya kuma koka ganin yadda rayuwar matashin ta zo karshe kwatsam, ‘yan kwanaki kadan bayan an sa shi a lalle.
Kwanaki 16 kafin aukuwar hadarin marigayin ya auri sahibarsa kuma abokiyar aiki, Lieutenant Damilola Adekunle.
A ranar 19 ga Satumba 2026, ‘yanuwa da abokon arziki da jami’an sojoji suka taru wurin auren shi da Damilola Adekunle.

Kara karanta wannan
Kasurgumin dan bindiga da yaransa 6 sun hadu da abin da ya fi ƙarfinsu, sun mutu nan take
Baya ga auren soja da yake yi, shi ma Marigayi Man-Ugwueje ya fito ne daga gidan sojoji.
Otti, a madadin iyalinsa da Gwamnati da mutanen jihar Abia, ya yi wa dangin marigayin da mutanen Umuahi da sojoji ta’aziyya.
Ya yi addu’a Ubangiji ya ji kan shi da sauran mamatan tare da rokon Ubangiji ya ba dangoginsu hakurin jure wannan babban rashi.
Vanguard ta fitar da bidiyon da aka dauka lokacin auren Ahamefule Aham Man-Ugwueje a watan Satumba.
Fama da hadarin jirgin sojoji
Kuna da labari cewa a tsakanin shekara ta 2021 zuwa 2026, an samu akalla hadarin jiragen sojin saman Najeriya har sau 10.
Bayanai sun tabbatar da cewa wadannan haduraa sun shafi jiragen yaki, na koyo, da masu saukar ungulu a wurare daban-daban.
Shugaba Bola Tinubu ya ayyana kwanaki uku na zaman makoki bayan hatsarin baya-bayan nan na jirgin ATR-42 a jihar Ondo.
Asali: Legit.ng
