INEC Ta Raba Gardama, Ta Fadi Matakin Dauka kan Jam'iyyun da Suka Karya Dokar Zabe
- INEC ta bayyana matakin da za ta dauka kan jam’iyyun da suka tsayar da ’yan takarar da ba sa cikin rajistar da aka gabatar mata
- Kotun Ƙoli ta tabbatar da ingancin wasu sassan Dokar Zaɓe ta 2026 da suka shafi rajistar ’yan jam’iyya da tsayar da ’yan takara
- Kwamishinan INEC Mohammed Haruna ya ce hukumar na nazarin hukuncin Kotun Ƙoli, kuma za ta iya bayyana matsayinta a mako mai zuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce jam’iyyun siyasa da aka gano sun tsayar da ’yan takarar da ba sa cikin rajistar da suka gabatar mata, ba za a bari su shiga zaɓen 2027 da waɗannan ’yan takara ba.
Hukumar INEC ta ce ba za ta kuma bari jam’iyyun su sauya irin waɗannan ’yan takara ba, domin hakan zai bai wa jam’iyyar damar cin moriyar abin da ta aikata wanda ya saɓa wa doka.

Source: Facebook
Kwamishinan INEC mai kula da yaɗa labarai da wayar da kan masu zaɓe, Malam Mohammed Haruna, ne ya bayyana hakan a cikin shirin Daily Politics na tashar Trust TV a yammacin Laraba, 7 ga watan Oktoban 2026.
INEC ba za ta amince da sauya ’yan takara ba
Mohammed Haruna ya ce jam’iyyun da suka karya tanadin doka wajen tsayar da ’yan takara ba za su samu damar sauya waɗannan ’yan takara ba.
Ya ce hakan zai zama kamar an bai wa wanda ya aikata laifi damar cin moriyar laifin da ya aikata.
“Kamar ka aikata laifi ne, sannan ka zo kana son cin moriyarsa. Kun tuna da wasu shari’o’in da muka samu a Zamfara, kun tuna da Plateau? Haka abin ya kasance,” in ji shi.
Haruna ya ce idan jam’iyya ta tsayar da ɗan takara wanda ba ya cikin rajistar jam’iyyar a lokacin da aka gudanar da zaɓen fitar da gwani, ba za a iya amfani da sauya ɗan takara wajen gyara wannan kuskuren ba.
Ya ce idan INEC ta kammala nazarin hukuncin Kotun Ƙoli, hakan na iya sa wasu jam’iyyun siyasa su kasa samun damar tsayar da ’yan takara a wasu matakan zaɓe.
Matsalar za ta iya shafar ’yan takarar gwamna
Kwamishinan ya ce matsalar ba ta tsaya ga ’yan takarar shugaban ƙasa ko sanatoci kawai ba, domin tana iya shafar ’yan takara har zuwa majalisun dokokin jihohi.
Ya ce INEC ta tattauna da ’yan takarar da jam’iyyun suka gabatar a matakai daban-daban, kuma an gano cewa kasancewa cikin rajistar jam’iyya na da muhimmanci wajen cancantar tsayawa takara.
“Dukkan ’yan takarar, har zuwa majalisun dokokin jihohi, mun tattauna da su. Idan sunayensu ba sa cikin rajistar jam’iyya, to ba mambobin jam’iyyar ba ne a lokacin da suka fafata neman tikitin,” in ji Haruna.
INEC na nazarin cikakken hukuncin Kotun Ƙoli
Haruna ya ce INEC ta fahimci cewa mutane da dama na cikin fargabar abin da hukuncin zai haifar, amma ya ce hukumar na buƙatar samun cikakken shawarar ƙwararrun lauyoyinta kafin ta bayyana matsayinta na ƙarshe.
Kwamishinan ya ce hukumar ta samu Certified True Copy (CTC) na hukuncin Kotun Ƙoli ranar Talata, kuma yanzu tana ci gaba da nazarinsa.

Kara karanta wannan
Zance ya kare: INEC ta yi magana kan hukuncin kotu da zai iya shafar takarar su Pantami
Ya ce INEC ba za ta yi gaggawar yanke hukunci ba saboda akwai yiwuwar a gabatar da takardun hukunci na bogi.
Haruna ya ce hukumar ta taɓa ganin wasu mutane suna da ƙarfin hali har su ƙirƙiro hukuncin Kotun Ƙoli na bogi, don haka dole ne ta tabbatar da sahihancin takardun kafin ta ɗauki mataki.
Ya ce INEC na fatan samun damar bayyana matsayinta na ƙarshe kan hukuncin zuwa Talata mai zuwa.

Source: Facebook
Kwamitin majalisa ya mika bukata ga INEC
A wani labarin kuma, kun ji cewa Kwamitin Majalisar Wakilai kan harkokin zaɓe ya mika bukatarsa ga hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC).
Kwamitin ya bukaci hukumar INEC ta hana ’yan takarar da sunayensu ba sa cikin rajistar mambobin jam’iyyunsu tsayawa takara.
Asali: Legit.ng

