El Rufai na Tsare, Sabon Rikici Ya Barke a Jam'iyyar ADC a Kaduna
- Magoya bayan Idris Mikati sun ƙi amincewa da takardar shaidar lashe zabe da ADC ta bai wa, Isa Ashiru Kudan
- Ƙungiyar ta ce takardar da aka bai wa Ashiru a ranar 4 ga Oktoba 2026 ta saɓa wa tsarin jam’iyyar da kuma dokokin da suka shafi rikicin cikin gida
- Mikati ya garzaya Babbar Kotun Tarayya da ke Maitama, Abuja, yana ƙalubalantar matakin tare da gargadin yiwuwar ƙarin shari’a idan aka aika sunan Ashiru zuwa INEC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Wata sabuwar takaddama ta kunno kai a reshen jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) na jihar Kaduna.
Takaddamar ta kunno ne bayan magoya bayan wani mai neman takara, Hon. Idris Shuaibu Abubakar Mikati, sun ƙi amincewa da takardar shaidar lashe zaben fitar da gwani da aka bai wa tsohon ɗan takarar gwamna, Hon. Isa Ashiru.

Source: Facebook
Ƙungiyar magoya bayan Mikati, wadda ta ƙunshi Kaduna State ADC Youth Vanguard da wasu ƙungiyoyin goyon baya daga ƙananan hukumomi 23 na jihar, ta bayyana hakan cikin wata sanarwa, cewar rahoton jaridar Leadership.
Ta bayyana takardar da aka bai wa Ashiru a ranar 4 ga Oktoba 2026 a matsayin wadda ba ta da inganci kuma ta saɓa wa tsarin da ya dace.
Magoya bayan Mikati sun ƙalubalanci takardar Ashiru
A cikin wata sanarwa da Usman Sani ya sanya wa hannu a madadin ƙungiyar, magoya bayan Mikati sun yi zargin cewa shugabannin ADC na ƙasa sun bayar da takardar ne duk da cewa akwai rikicin cikin gida da kuma shari’a da ke gudana kan zaɓen fitar da gwani na gwamna da jam’iyyar ta gudanar a Kaduna a watan Mayu 2026.
Wannan mataki ya sake buɗe takaddamar da ta dabaibaye sakamakon zaɓen fitar da gwani, inda aka ayyana Ashiru Kudan a matsayin wanda ya yi nasara da ƙuri’u 86,113.

Kara karanta wannan
Kotun daukaka kara ta shirya yanke hukunci a bukatar da El Rufai ya dade yana nema
An ce kwamitin ɗaukaka ƙara ya sauya sakamakon
A cewar ƙungiyar, ’yan takara huɗu da ba su gamsu da sakamakon ba, ciki har da Mikati, sun ƙalubalanci sakamakon a gaban Kwamitin Ɗaukaka Ƙara na Zaɓen Fitar da Gwani na jam’iyyar.
Kwamitin, wanda Dr Mustapha Fagge ya jagoranta, ya sake nazarin koke-koken da hujjojin da aka gabatar masa.
Ƙungiyar ta yi zargin cewa kwamitin ya soke nasarar da aka bai wa Ashiru, sannan ya ayyana Mikati a matsayin sahihin ɗan takarar ADC na gwamna a Kaduna.
Sai dai ƙungiyar ta ce Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) bai tattauna tare da tabbatar da rahoton kwamitin ɗaukaka ƙarar ba.
An zargi NWC da rashin zama na tsawon watanni
Magoya bayan Mikati sun kuma yi zargin cewa NWC, wanda ke da alhakin gudanar da harkokin jam’iyyar na yau da kullum, bai gudanar da taro na tsawon sama da watanni shida ba.
A cewar ƙungiyar, duk da wannan yanayin ne aka bayar da takardar ga Ashiru ba tare da warware saɓanin matsayar da ya taso daga zaɓen fitar da gwanin ba.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Uba Sani ta fadi abu 2 da suka fi rashin tsaro barazana ga zaman lafiya
“Ta yaya jam’iyya za ta kafa tsarin warware rikicin cikin gida sannan ta yi watsi da hukuncin da nata tsarin ya yanke?” ƙungiyar ta tambaya.
Ta bayyana bayar da takardar ga Ashiru a matsayin matakin da aka ɗauka ba tare da bin tsarin da ya dace ba.
An ƙi amincewa da takardar Ashiru Ƙungiyar ta ce ta ƙi amincewa da takardar da aka bai wa Ashiru, tana mai cewa ba ta da wani tasiri saboda, a cewarta, babu sahihin hukuncin NWC ko Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) da ya tabbatar da rahoton kwamitin ɗaukaka ƙara.
Ta nemi shugabannin ADC na ƙasa da su janye matakin, su kira taron gaggawa na NWC sannan su sake duba rahoton Kwamitin Ɗaukaka Ƙara da Dr Mustapha Fagge ya jagoranta.
Mikati ya garzaya kotu
Ƙungiyar ta ce Mikati ya garzaya Babbar Kotun Tarayya da ke Maitama, Abuja, domin ƙalubalantar matakin da aka ɗauka.
Ta kuma yi gargadin cewa duk wani yunƙuri na aika sunan Ashiru zuwa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) domin ya zama ɗan takarar jam’iyyar a zaɓen 2027 na iya haifar da ƙarin ƙalubalen shari’a.

Source: Original
ADC ta gargadi INEC
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam’iyyar ADC na ƙasa, David Mark, ya ce jam’iyyar za ta bi ƙa’idojin zaɓe a babban zaɓen 2027, amma ba za ta yarda da yunƙurin yi mata magudi ko hana ta nasara ba.
Mark ya ce ADC ta himmatu wajen gudanar da harkokin siyasarta ta yadda za ta ƙara wa jama’a kwarin gwiwa kan tsarin dimokuraɗiyya.
Asali: Legit.ng

