Kisan gilla: Iyalan Janar Murtala sun bukaci adalci daga gwamnatin Najeriya

Kisan gilla: Iyalan Janar Murtala sun bukaci adalci daga gwamnatin Najeriya

Iyalan marigayi tsohon shugaban kasar Najeriya, Marigayi Janar Murtala Muhammad a ranar juma'ar da ta gabata sun yi kira ga gwamnatin tarayya musamman ma 'yan majalisa dasu tabbatar da dabbaka dokar kare hakkin wanda aka zalunta.

Aisha Muhammed Oyebode dake zaman daya daga cikin 'ya'yan marigayin ce tayi wannan kiran a garin Legas a lokacin da suke yin taron tunawa da dan kanin su da aka kashe kimanin shekaru 25 da suka gabata mai suna Zakari Muhammad.

Kisan gilla: Iyalan Janar Murtala sun bukaci adalci daga gwamnatin Najeriya

Kisan gilla: Iyalan Janar Murtala sun bukaci adalci daga gwamnatin Najeriya

KU KARANTA: Malaman Arewa sun shirya yadda za su kawo karshen shi'a

Legit.ng ta tuna cewa shima dai mahaifin nasu Janar Muratala Muhammad kashe akayi lokacin yana shugaban kasa kafin kuma daga baya a kashe dan nasa.

A wani labarin kuma, 'Yan sandan Najeriya shiyyar jihar Oyo sun sanar da samun nasarar cafke wani mutum mai mai suna Olayinka Emmanuel mai kuma shekaru 54 a duniya da yayi ikirarin shi farfesa ne a jami'ar gwamnatin tarayya dake a garin Ibadan.

'Yan sandan dai sun bayyana cewa sun samu nasarar cafke shi ne bayan da yayi kokarin damfarar wani mutum a garin zunzurutun kudi har Naira miliyan daya da zummar hada masa wani maganin dabbobi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel