Jaruman da suka fara yakin Biyafara a Najeriya sun kasance masu butulci – Obasanjo

Jaruman da suka fara yakin Biyafara a Najeriya sun kasance masu butulci – Obasanjo

- Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana butulcin Odugmegwu Ojukwu a matsayin abunda ya haddasa yakin Biyafara

- Obasanjo ya bayyana hakan ne a gurin tunawa da hadin kai, Biyafara bayan shekaru 50

- Tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa dukkan jami’an da suka fara yakin basasan Najeriya na 1967 sun kasance masu butulci

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa dukkan jami’an da suka fara yakin basasan Najeriya na 1967 sun kasance masu butulci.

Da yake magana a gurin taron tunawa da hadin kai Biyafara bayan shekaru 50 wato “Memory and Nation Building, Biafra: 50 Years After”, tsohon shugaban kasar ya ce dukkan jami’an da suka fara yakin a 1967 sun kasance butulu kuma basu taba sanin abunda suke shirin shiga ba.

"Ko da yake akwai wasu kishin kasa a tattare da wasun su. Sannan kuma wannan ne ya ajiye mu a inda muke a yanzu.” Cewar Obasanjo.

Jaruman da suka fara yakin Biyafara a Najeriya sun kasance masu butulci – Obasanjo
Obasanjo ya ce Jaruman da suka fara yakin Biyafara a Najeriya sun kasance masu butulci

Ya ci gaba da yin Allah wadai da ayyukan wasu shugabannin Najeriya wadanda ke tursasa kiyayya a zukatan al’umman Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Obasanjo, Osinbajo da sauran su sun tattauna a kan Biyafara bayan shekaru 50 a Abuja

“Bamu da shugabannin kasa, muna da shugabanni ukku a farkon tafiyar mu a matsayin kasa wadanda suke da tunanin yankunan su. Matsalar mu kenan.

A lokacin da ka saurari shugabannin mu suna magana game da yancin kai sannan kuma babu hadin kai a yankin su."

Obasanjo ya ce dukkan jami’an da suka yi yakin basu taba ganin kawunan su a matsayin makiya ba.

“Muna kallon yan uwanmu a dayan bangaren a matsayin yan tawaye, bamu taba kiran junanmu da makiya ba.

"Na fada a baya, yakin basasa ya kasance yaki mafi wahala yaki da kasar waje.

"Mun so mu kare kasarmu ne, sasanci shine a zukatanmu,” Inji Obasanjo.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng