Asiri Ya Tonu: An Kama Wanda Ya Hada Maganin da Ya Kashe Mutane da Yawa a Najeriya
- ’Yan sanda sun kama wani mutum da ake zargi da hada maganin garhajiyan da ke da alaƙa da mutuwar mazauna Araromi-Obu da Odigbo
- Rahotanni sun ce aƙalla mutane 29 sun mutu yayin da wasu kusan 60 ke kwance a asibiti bayan shan maganin
- An kuma kama wasu mutane 14 da ake zargi da sayarwa da shan magungunan duk da dokar hana amfani da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ondo, Nigeria - Rundunar ’yan sandan Ondo ta kama wanda ake zargi da hada maganin gargajiya da ake kyautata zaton yana da alaƙa da mutuwar mutanen kauyukan Araromi-Obu da Odigbo da ke ƙaramar hukumar Odigbo.
Yan sanda sun bayyana wanda ake zargin da suna Oloruntoba Babatunde, wanda aka fi sani da “Meko”.

Source: Twitter
An kama masu sayar da magani
Jaridar Leadership ta rahoto cewa an kama shi ne bayan rahotannin cewa aƙalla mutane 29 sun mutu, yayin da wasu kusan 60 aka kwantar a asibiti bayan zlsun sha wannan magani.
Rundunar ta kuma kama wasu mutane 14 bisa zargin sayarwa da shan magungunan ganye, duk da dokar da aka sanya ta hana sayarwa da shan magungunan a yankin.
A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Abayomi Jimoh, ya fitar ranar Litinin, ya ce rundunar ta shawo kan lamarin bayan ɗaukar matakan tsaro, kiwon lafiya da bincike na tsawon lokaci.
Jimoh ya ce ana zargin Babatunde da haɗa wasu abubuwa da ake kyautata zaton suna ɗauke da sinadarin methanol, kuma a yanzu yana taimaka wa ’yan sanda wajen gudanar da bincike.
Ya ce an kuma kwato wasu abubuwa da ake zargin sinadarin methanol ne daga hannun wanda ake zargin, kuma an tura su domin ƙarin bincike da gwaje-gwajen domin gano ainihin abin da suka ƙunsa.
Bincike kan mutuwar jama’a a Ondo
Sanarwar ta ce:
“Rundunar ’yan sandan Ondo ta shawo kan lamarin da ya biyo bayan mutuwar matasa kwatsam a a Araromi-Obu, ƙaramar hukumar Odigbo ta jihar, bayan ɗaukar matakan tsaro, kiwon lafiya da bincike na tsawon lokaci.
“Lamarin ya biyo bayan kama Oloruntoba Babatunde, wanda aka fi sani da ‘Meko’, wanda ake zargi da hannu wajen haɗa wasu abubuwa da ake kyautata zaton suna ɗauke da sinadarin methanol.

Source: Original
Kakakin ’yan sandan ya ce an fara bincike kan abubuwan da suka haifar da mutuwar mutanen, yana mai cewa ana gudanar da bincike kan gawarwakin waɗanda suka mutu.
A cewarsa, ana sa ran sakamakon gwaje-gwajen gawarwakin zai samar da ƙarin shaida kan ainihin musabbabin mutuwar, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Yadda maganin ya kashe mutane a Ondo
Tun farko, kun ji cewa akalla mutane 24 sun mutu a wasu garuruwa biyu da ke ƙaramar hukumar Odigbo a jihar Ondo, bayan sun sha wani maganin gargajiya.
Wasu mazauna yankunan da suka sha ruwan maganin sun kuma samu matsala, inda ake ci gaba da ba su magani a asibitoci daban-daban.
Rahotanni sun daga baya wadanda suka mutu sun karu zuwa 29, lamarin da ya ja hanaklin hukumomi, wadanda suka kaddamar da bincike.
Asali: Legit.ng

