Gwamna Uba Sani Ya Fadi Sirrin Kawo Karshen Zubar da Jini a Kaduna

Gwamna Uba Sani Ya Fadi Sirrin Kawo Karshen Zubar da Jini a Kaduna

  • Gwamnan Kaduna, Uba Sani ya bayyana cewa jiharsa ta samu raguwar rikice-rikicen kabilanci ko na addini a cikin shekarun biyun da suka wuce
  • Gwamnan ya danganta kwanciyar hankali da muhimmancin rawar da shugabannin gargajiya ke takawa wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya
  • Ya fadi haka ne a wajen raba motoci ga shugabannin gargajiya a Kaduna, wanda gwamnan ya bayyana da cewa zai taimaka a tattara bayanan tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna - Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya bayyana cewa jihar ba ta samu wani rikici na kabilanci ko na addini a cikin shekaru biyu da suka wuce ba.

Ya bayyana cewa rashin rikice-rikice a jihar na daga cikin sakamakon rawar da shugabannin gargajiya ke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya.

Gwamna
Gwamna Uba Sani ya ce an samu raguwar rikicin addini da kabilanci a Kaduna Hoto: Senator Uba Sani
Asali: Facebook

The Cable ta wallafa cewa Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin rarraba motoci 23 ga shugabannin gargajiya a gidan Sir Kashim Ibrahim a ranar Lahadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ake magance rashin tsaro a Kaduna

Daily Trust ta ruwaito cewa Gwamna Uba ya nuna cewa suna aiki tukuru, suna musayar bayanai tare da jami'an tsaro, da kuma kula da tsaron mazauna jihar,

Ya ce:

"Shi ya sa dabarar rashin amfani da karfi wajen magance rashin tsaro ta yi tasiri. Idan ba tare da goyon bayan shugabannin gargajiya ba, ba za mu iya samun kwanciyar hankali da tsaro da muke jin dadinsa a jihar Kaduna yau ba."

Gwamnan Kaduna ya jaddada muhimmancin hadin kai tsakanin cibiyoyin gargajiya, shugabannin addini, shugabannin al'umma da hukumomin tsaro don wanzuwar zaman lafiya.

Gwamnan Kaduna ya yaba da shugaban majalisa

Gwamna Uba Sani ya jinjinawa shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas a kan yadda ya waiwayi sarakunan gargajiya a jihar Kaduna.

Ya ce an raba motoci ne ga shugabannin gargajiya domin ya kara masu kwarin gwiwa, ya jaddada muhimmancin rawar da suke takawa wajen tattara bayanan sirri da kuma musayar su.

Abbas
Shugaban majalisar wakilan Najeriya, Tajudeen Abbas Hoto: Tajudeen Abbas
Asali: Facebook

A nasa bangaren, shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas ya ce an raba motocin ta hannun Hukumar Ci gaban Kanana da Matsakaitan Masana'antu (SMEDAN).

Ya bayyana hakan a matsayin wani bangare ne na shirin rarraba motocin a mataki na hudu na domin karfafawa sarakunan yankin.

Rt. Hon Tajudeen ya ce motocin za su zama tamkar kayan aiki da za su taimaka wa shugabannin gargajiya wajen zuwa dukkanin yankunan masarautarsu don kara wanzar da zaman lafiya.

'Yan bindiga sun kutsa kauyen Kaduna

A baya, kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun sace Harira Abdullahi, matar Hakimin Aboro da ke ƙaramar hukumar Sanga a Jihar Kaduna, tare da 'yarta Maryam Suleiman Galadima.

Rahotanni sun ce miyagun 'yan bindigan sun kutsa cikin gidan hakimin da misalin ƙarfe 7:36 na yamma, suka yi awon gaba da matarsa da 'yarsa ba tare da sun fuskanci wata barazana ba.

Bayan sace matan, mazauna garin sun yi ƙoƙarin bin 'yan bindigan cikin daji domin ceto su. Sai dai hakan ya jawo mummunar asara, aka kashe wani daga cikin masu kokarin ceto su, Umar Abdullahi, wanda aka harbe har lahira.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.