EFCC Za Ta Binciki Atiku da Ministan Buhari kan Badakalar Aikin Wutan Mambilla

EFCC Za Ta Binciki Atiku da Ministan Buhari kan Badakalar Aikin Wutan Mambilla

  • Shugaban hukumar EFCC ne yake jagorantar kwimiti na musamman domin tabbatar da an yi bincike mai zurfi kan badakalar aikin wutan Mambilla
  • Wannan bincike ya biyo bayan nasarar da Najeriya ta samu a kotun ICC a kan kamfanin Sunrise Power, aka yi watsi da neman biyan dalolin kudi
  • Bayanan ICC sun jefa jami'an gwamnati da dama a matsala, Olanipekun Olukoyede zai binciki irinsu Atiku Abubakar da tsohuwar matarsa a EFCC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - EFCC mai yaki da rashin gaskiya ta kafa wani kwamiti da zai binciki wadanda sunansu ya fito a badakalar akin wutan Mambilla.

Akwai wadanda ake zargi suna da hannu a wasu nugayen yarjejeniyoyi da kamfanin Sunrise Power and Transmission Company Ltd.

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar a wajen Abubakar Malami SAN Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Kwamitin EFCC zai binciki badakalar aikin Mambilla

Wani rahoto na musamman da ya fito daga Premium Times ya ce shugaban EFCC, Olanipekun Olukoyede yake kula da aikin kwamitin.

Kara karanta wannan

ICC ta saki yadda minista ya nemi yaudarar Buhari a ci $200m a aikin Mambilla

An kafa kwamitin da zai yi binciken ne sakamakon nasarar da Gwamnatin Najeriya ta samu a kan kamfanin Sunrise da aka je ICC a Faransa.

ICC ya hada Atiku, Malami, Dasuki da aiki

Sunayen wasu manya a Najeriya ya fito a cikin wadanda suka yi hulda da Leno Adesanya wanda aka yi ta shari’a da kamfaninsa a kotu.

Cikin wadanda lambobin su suka fito akwai Atiku Abubakar da matarsa a lokacin Jennifer Douglas da kuma Abubakar Malami SAN.

Akwai Olu Agunloye, Sambo Dasuki da ‘dansa, Abubakar Dasuki, Abdullahi Yola, da Dere Awosika.

Ban da rawar da Malami ya taka a shari’a kan aikin wutan Mambilla, EFCC tana karar shi da matarsa da ‘dansa kan mallakar dukiyar N8.7bn.

An ji rawar da Atiku ya taka na $500, 000 da Adesanya ya biya a 2003 zuwa kamfanin tsohuwar matar shi, China Castle Investments Ltd.

ICC ta ce an biya kudin ne watanni kafin sa hannu a yarjejeniyar gyaran wutan Mambila a lokacin Mista Olu Agunloye yana ministan makamashi.

Kara karanta wannan

Atiku ya kare kansa daga sabon zargin da APC ta masa da neman hakura da takara

Rahoton ya ce makudan dalolin sun shiga wani kasuwanci canjin kudi da Alhaji Atiku yake yi.

Sai dai ICC ta ce babu hujjar da ke nuna Atiku ya yi umarni da kan shi ko ta hannun hadiminsa cewa ya bukaci kudi wajen tsohon ministan kasar.

Haka kuma ba a samu hujja ko shaida ko wasu takardu da za su tabbatar da zargin ba duk da akwai alaka tsakanin Atiku da Agunloya a sannan.

Inda Sambo Dasuki da wasu suka fito

Dama shi Mr Agunloye yana kotu a yanzu, gwamnati tana tuhumarsa da laifuffuka har bakwai.

Shi kuwa Sambo Dasuki, an nemi jin yadda mutanen kamfanin Sunrise Power suka aika wa ‘dan shi, Abubakar Dasuki da kudi har $1.74m.

Ana zargin wani jami’i, Abdullahi Yola da babban sakatare a ma’aikatar wuta, Dere Awosika da cin hanci da karbar kudi da ke da alamar tambaya.

Hukumar EFCC za ta iya gayyato Atiku

Majiya ta ce akwai yiwuwar nan da ‘yan makonni EFCC ta gayyaci Atiku da tsohuwar mai dakinsa, Douglas domin su amsa wasu tambayoyi.

Kara karanta wannan

Zargin cin kudi ya kai ‘dan takaran APC a zaben majalisa cikin ragar hukumar ICPC

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya tabbatar da cewa ya san da wannan magana a kasa.

Atiku ta bakin hadiminsa, Phrank Shaibu, ya yi watsi da zargin, yana mai cewa a nuna hujjar cewa ya karbi cin hanci ko ya ci amanar ofishinsa.

Abubakar Malami
Abubakar Malami lokacin yana ministan shari'a Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An zargi Malami da neman kudi a yarjejeniyar Mambilla

A game da aikin Mambilla, ana da labari Abubakar Malami ya so ya yaudari Muhammadu Buhari lokacin yana minista domin a biya karin kudi.

Kotun ICC ta jefa ministocin Muhammadu Buhari biyu a matsala dangane da rikicin kamfanin Sunrise a kwangilar Mambilla ta yadda za a ci $200m.

Wani ministan da sunan shi ya fito a lamarin shi ne Saleh Mamman, wanda kotu ta same shi da laifi a wata shari'a ta dabam da aka yi a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng