Akwai Matsala: 'Yar Amurka Ta Goge Sakonnin da Ta Fitar kan Tinubu da Najeriya

Akwai Matsala: 'Yar Amurka Ta Goge Sakonnin da Ta Fitar kan Tinubu da Najeriya

  • Masaniyar siyasa kuma mai sharhi kan harkokin yaɗa labarai a Amurka, Diana London, ta goge saƙonnin da ta wallafa a shafinta
  • A baya ta wallafa hotunanta a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja tare da Shugaba Bola Tinubu da shugaban ma'aikatan fadar, Femi Gbajabiamila
  • London ta kuma bayyana haɗin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka a matsayin wanda ke samar da sakamako mai kyau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Amurka - Sa'o'i kadan bayan ta wallafa hotunanta da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, masaniyar dabarun siyasa kuma mai sharhi kan harkokin yaɗa labarai a Amurka, Diana London, ta sauya shawara ta goge sakonnin.

Fitacciyar yar kasar Amurka ta goge sakonnin da ta wallafa sakonningame da hulɗarta da gwamnatin Najeriya da kuma haɗin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka, inda aka ce ta yi hira da Tinubu.

Kara karanta wannan

Da gaske Majalisar Amurka ta zaɓi wanda take goyon baya a zaben Najeriya? Bayanai sun fito

Diana London.
Masaniyar harkokin siyasa daga kasar Amurka, Diana London tare da Shugaba Bola Ahmed Tinubu Hoto: Imran Muhammad
Source: Facebook

Punch ta rahoto cewa a baya, London ta wallafa hotunanta a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda aka gan ta tare da Shugaba Bola Tinubu da shugaban ma'aikatan fadar, Femi Gbajabiamila.

Sakonnin da Diana London ta wallafa

Haka kuma, an ga kyamarori a wasu daga cikin hotunan. A wani saƙon kuma, ta bayyana haɗin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka a matsayin wanda ke “samar da sakamako”.

Ta rubuta cewa:

“Haɗin gwiwar tsaro tsakanin Amurka da Najeriya na samar da sakamako mai kyau da zaman lafiya.
"Babu ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa da zai yiwu ba tare da haɗin gwiwar da ke gudana tsakanin Shugaba Trump da Shugaba Tinubu, jajircewarsu wajen kawar da 'yan ta'adda, da kuma shirye-shiryen Najeriya na yin aiki kafada da kafada da gwamnatin Amurka ba.”

Diana London ta kuma nuna cewa haɗin gwiwar na iya buɗe ƙarin damammaki a fannin tattalin arziki da kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya yi hira da fitacciyar 'yar Amurka, za a saki bidiyon tattaunawar

Ta bayyana cewa:

“Saboda nasarar haɗin gwiwarsu da kyakkyawar alaƙar da ke tsakaninsu, damammakin tattalin arziki da kasuwanci sun bude kuma ba su da iyaka. Abubuwa mafi kyau suna nan tafe. Najeriya ita ce babbar ƙawar Amurka a Afirka.”

Diana London ta yaba da haɗin gwiwar

A wani saƙo na daban, London ta bayyana jin daɗinta kan damar yin aiki tare da mutanen da ke wakiltar Najeriya, musamman wajen ƙoƙarin kare ƙungiyoyin addinai da ƙarfafa alaƙa tsakanin gwamnatin Shugaba Trump da gwamnatin Najeriya.

Ta rubuta cewa:

“Abin alfahari ne a gare ni na kasance cikin tawagar mutanen da ke wakiltar Najeriya, tare da taimakawa wajen kare ƙungiyoyin addinai da kuma ƙara ƙarfafa alaƙa tsakanin gwamnatin Trump da gwamnatin Najeriya.”
London.
Fitacciyar yar Amurka, Diana London da tawagarsa lokacin da suka kai ziyara fadar shugaban kasa da ke Abuja Hoto: Imran Muhammad
Source: Facebook

Ta goge duka sakonnin a shafinta

Sai dai, ya zuwa safiyar ranar Laraba, lokacin da wakilin Punch ya duba shafinta na X, an riga an goge waɗannan saƙonni.

Har yanzu ba a bayyana dalilin da ya sa aka cire saƙonnin ba, kuma London ba ta yi wani bayani a bainar jama'a kan dalilin goge su ba.

Kara karanta wannan

2027: Sanatan Kano ya faɗawa Tinubu gaskiya kan ƙalubalen da APC za ta fuskanta a Arewa

Tinubu ya yi hira da Diana London

Kun ji cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata hira ta musamman da fitacciyar masaniyar siyasa kuma mai sharhi kan kafafen yada labarai ta Amurka, Diana London.

Ana sa ran za a fitar da hirar nan ba da jimawa ba, kamar yadda wani hadimin shugaban APC na kasa ya bayyana a wata sanarwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262