Jami’in Tsaro Ya Rasa Aikinsa a ICPC daga Kyale Matar El Rufai Ta Gan Shi a Tsare

Jami’in Tsaro Ya Rasa Aikinsa a ICPC daga Kyale Matar El Rufai Ta Gan Shi a Tsare

  • ICPC ta sallami jami’in tsaro bayan na'urar CCTV ta nuna shi yana taimakawa matar Nasir El-Rufai ta gan shi
  • Jami'in ya amsa laifinsa inda ya tabbatar da cewa ya shigar da matar ta kofar baya a lokacin da ba na ziyara ba
  • Yanzu Daniel Stephen ya rasa aikinsa bayan ya amsa laifinsa, ana zargin ya saba ka’idar fiye da sau daya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - ICPC mai yaki da cin hanci da rashawa ta kori wani jami’in tsaro a dalilin tirka-tirkar da ake yi da Malam Nasir El-Rufai.

Hukumar ICPC ta sallami wannan ma’aikaci ne saboda ya ba Aichatou Assabe El-Rufai damar ganin Malam Nasir El-Rufai.

Nasir El-Rufai
Nasir El-Rufai da Aichatou Assabe El-Rufai Hoto: Hoto: Abubakar MK Gwantu
Source: Facebook

Jami'in ICPC ya rasa aiki a dalilin Aichatou El-Rufai

Wani rahoto da aka gani a jaridar The Cable ya ce ana zargin jami’in ya bari Aichatou El-Rufai ta ga mijinta ba tare da hurumi ba.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Ministan tsaro ya yi zarge zarge kan El Rufa'i da ke tsare

An ce an ga Daniel Stephen a na’urar CCTV yana taimaka wa Aichatou El-Rufai ta ga mijinta a lokacin da ba na kawo ziyara ba.

Kamar yadda shi Mista Daniel Stephen ya fada a rubutun da ya yi da hannunsa, abin ya faru ne a ranar Lahadi, 5 ga Yuli 2026.

Stephen wanda ke aikin gadin cikin hukumar ICPC ya amsa laifin cewa ya taimaka wa matar ta ga mijinta ta hanyar bi ta kofar baya.

Yadda aka saci hanyar ganin Nasir El-Rufai

Majiya ta ce mai gadin ya shiga da Hajiya Aichatou Assabe El-Rufai cikin harabar ICPC, daga nan yabi ta ita ta baya har ta hau bene.

Daga benen ne ta je har sama inda mai gidanta yake tsare, ba tare da jami'ai sun ankara ba.

Kamar yadda wani jami’in hukumar ICPC ya sanar da jaridar, kafin ta shiga dakin da aka ajiye El-Rufai, Stephen ya kashe wutar.

Kara karanta wannan

Magidanta za su iya zuwa gidan yari kan aukawa matansu ba tare da yardarsu ba

"Matar El-Rufai ta ba mai gidanta wata takarda, ta karbi wata bakar alabe kuma ta yi magana da shi game da zancen shari'a a kotu."
"Ziyarar ta shafe kusan mintuna 15."

Daga nan sai kuma jami’in tsaron ya sake jan ta suka bi ta kofar baya, suka fice daga harabar hukumar ta yadda ba za a gan ta ba.

Jami'in ICPC ya amsa laifinsa da kansa

Business Day ta ce jami’in ya rubuta da hannunsa cewa ya yarda ya saba dokar aikinsu na ICPC.

Kamar yadda ya rubuta da hannunsa, ya ce ya yi wannan aiki ne ba tare da tursasawa ko matsin lamba, ganin damarsa ce kawai.

A ka’ida duk wanda zai shiga wurin sai ya samu izini daga shugaban sashen tsaro a bakin kofar shiga kuma sai an dauki bayaninsa.

Ban da matar, ana zargin ya taba taimaka wa danuwan El-Rufai ya gan shi ta irin wannan haramtacciyar hanya, aka bi ta kofar baya.

Nasir El-Rufai
Tsohon gwamna Nasir El-Rufai zai shiga kotu Hoto: Nasir El-Rufai
Source: Facebook

TX

El-Rufai ya ce an hana shi ganin iyali

An ji labarin yadda Nasir El-Rufai ya koka cewa hukumar ICPC ta hana shi gana wa da iyalinsa, a kan wannan ya yi kara gaban kotu.

Kara karanta wannan

Majalisar shari’a ta gaji da ganin yadda aka tsare El Rufai ta kai an soma magana

Hajiya Aichatou Assabe El-Rufai ita ce matar tsohon gwamnan ta hudu, ta yi ta kokarin kai masa ziyara da yake a tsare, har ana hana ta.

Tun a Fubrairun 2026 ake tsare da tsohon gwamnan Kadunan bisa zargin wanke kudin haram da wasu laifuffuka lokacin yana ofis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng