"Bana Son A Kara Kirana wanda Ya Fi Ko Kudi a Afrika"; Dangote Ya Fadi Sunan da Yake So
- Aliko Dangote ya bayyana cewa baya son a rika kiran shi attajirin za ya fi kowa kudi a nahiyar Afrika
- Ya bayyana cewa burinsa shi ne ya samar da arziki ga sauran mutane ta hanyar saka hannun jari da bunƙasa kasuwanci
- Kamfanin matatar Dangote ya ƙaddamar da sayar da hannayen jarinsa 4.1bn a kasuwar hannayen jari ta Najeriya kan N525 kowanne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Legas - Shugaban rukunin kamfonin Dangote, Aliko Dangote, ya ce ba ya son a ƙara kiransa mutumin da ya fi kowa kudi a Afirka.
Dangote ya bayyana cewa ya fi son a san shi a matsayin attajirin da ke taimakawa wajen samar da arziki ga wasu.

Source: Getty Images
The Punch ta ce attajirin ya bayyana hakan ne ranar Litinin, 14 ga watan Satumban 2026 yayin da yake kaddamar da sayar da hannayen jarin matatar Dangote a Legas.
“Ina son samar da arziki ga wasu”
Dangote ya ce bai damu da yadda ake kallon girman dukiyarsa ba, sai dai yana son dukiyar da ya samu ta yi amfani wajen samar da ƙarin arziki ga sauran mutane.
“Ba na son kowa ya sake kirana mutumin da ya fi kowa kudi a Afirka. Ina son a kira ni attajirin da ya fi kowa arziki a Afirka, domin na samar da arziki ga wasu,” in ji shi.
Ya bayyana sayar da hannayen jarin matatar a matsayin wata dama da masu zuba jari za su samu domin kasancewa cikin wani sabon babi na ci gaban tattalin arzikin Najeriya da Afirka.
Dangote ya yi kira kan kasuwar hannayen jari
Hamshakin ɗan kasuwar ya yi kira ga ’yan Najeriya da su ƙara shiga kasuwar hada-hadar hannayen jari tare da bunƙasa tsarin da zai bai wa mutane da dama damar mallakar wani ɓangare na arzikin ƙasa.

Kara karanta wannan
Zaben 2027: Ma'aikata za su huta, dan takara ya yi alkawarin biyan mafi karancin albashin N500,000
Ya ce hakan zai taimaka wajen samar da wadata da kuma ƙarfafa tattalin arzikin Najeriya da Afirka baki ɗaya.
Ya ambaci sadaukarwar da ya yi wa kasuwanci
Dangote ya kuma yi magana kan irin sadaukarwar da ya yi tsawon shekaru domin gina daular kasuwancinsa.
Ya ce ya shafe shekaru da dama yana kasancewa nesa da iyalansa saboda ayyukan kasuwanci.
Ya gode wa ’ya’yansa mata uku, Mariya, Halima da Fatima, bisa fahimta da goyon bayan da suka nuna masa a tsawon wannan lokaci.
Matatar Dangote ta fara sayar da hannayen jari
An fara sayar da hannayen jarin ne ranar Litinin, 14 ga Satumba, 2026, inda aka fitar da sabbin hannayen jari biliyan 4.1 na matatar Dangote.
Ana sa ran za a rufe sayar da hannayen jarin ranar 13 ga Oktoba, 2026, bisa sharuddan da ke cikin takardar bayanan sayar da hannayen jarin.

Source: Facebook
Dangote ya yi magana kan matatarsa
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kamfanin Dangote, Aliko Dangote, ya yi tsokaci kan shirin sayar da hannun jari a matatarsa.
Dangote ya ce hannayen jarin matatar man Dangote da ake bayarwa kan N525 kowanne na iya kaiwa N10,000 nan gaba.
Asali: Legit.ng
