MURIC Ta Tsoma Baki, Ta Fadi Matsayarta kan Harin da Aka Kai Wa Sheikh Musa Lukuwa

MURIC Ta Tsoma Baki, Ta Fadi Matsayarta kan Harin da Aka Kai Wa Sheikh Musa Lukuwa

  • Kungiyar MURIC ta yi Allah wadai da harin da aka kai wa Sheikh Musa Lukuwa da kuma zargin kashe wanda ake zargi da kai harin
  • Ƙungiyar ta ce babu wani tsokana ko saɓanin addini da zai halasta tashin hankali ko kashe mutum ba tare da bin doka ba
  • MURIC ta kuma ce wasu kalaman da ake zargin Sheikh Lukuwa ya yi na iya haifar da tashin hankali a jihar Sokoto

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto - Ƙungiyar Kare Hakkin Musulmi ta Najeriya (MURIC), reshen jihar Sokoto, ta yi Allah wadai da harin da aka kai wa malamin addinin Musulunci, Sheikh Musa Lukuwa bayan sallar Juma'a.

Haka zalika MURIC ta yi tir da daukar matakin kashe wanda ake zargi da dabawa malamin wuka da wasu fusatattun mutane suka yi.

Kara karanta wannan

Musulmai sun ɗauki mataki mai tsauri da aka gano yan bindiga na shirin kai hari masallatai

Lukuwa.
Babban malamin addinin musulunci a jihar Sakkwato, Sheikh Musa Lukuwa Hoto: Sahalu Musa Lukuwa
Source: Facebook

Daily Trust ta bayyana cewa MURIC ta fadi haka ne a cikin wata sanarwa da wakilinta, Dr Muhammad Mansur Aliyu, ya sanya wa hannu.

MURIC ta yi Allah wadai da lamarin

Ta ce babu wani tsokana ko saɓanin addini da zai iya zama hujjar yin tashin hankali ko kashe mutum ba tare da bin tsarin shari'a ko doka ba.

Sai dai ƙungiyar ta nuna kuma damuwa da wasu kalamai na baya-bayan nan da ake dangantawa da Sheikh Lukuwa, waɗanda ta bayyana a matsayin wadanda ja iya haifar da tashin hankali a jihar.

A cewar MURIC, ta samu faifan bidiyo na wasu kalamai da ake zargin malamin ya yi, ciki har da kalaman da suka shafi matsayin iyayen Annabi Muhammad (SAW), kabarin Sheikh Usman Dan Fodiyo, Sarkin Musulmi, da sauransu.

Ta ce bai kamata a yi watsi da irin waɗannan kalamai kawai a matsayin saɓanin fahimtar addini ko ‘yancin faɗar albarkacin baki ba idan har za su iya zama barazana ga zaman lafiyar jama’a.

Kara karanta wannan

'Ban taɓa fitar da Zakkah ba': Sarkin Zazzau ya faɗi abin da ya fi ba muhimmanci

“‘Yancin addini yana zuwa ne tare da alhakin kauce wa tunzura jama’a, zagi, tsokana da kalaman da za su iya yin barazana ga zaman lafiyar jama’a,” in ji ƙungiyar.

MURIC ta soki hukumomin tsaro

MURIC ta kuma soki hukumomin tsaro da na gwamnati bisa zargin gaza ɗaukar matakan da suka dace tun da wuri kan abin da ta bayyana a matsayin kalamai masu kawo cece-ku-ce da malamin ya riƙa yi.

Ta ce da a ce hukumomin tsaro da abin ya shafa sun gayyaci malamin domin neman ƙarin bayani, ba shi shawara da kuma gargaɗe shi kan illar da ka iya biyo bayan wa’azinsa.

Sai dai ƙungiyar ta jaddada cewa ko da gwamnati ko hukumomin tsaro sun gaza ɗaukar mataki, hakan bai bai wa kowa damar ɗaukar doka a hannunsa ba.

Sokoto.
Taswirar jihar Sakkwato da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ƙungiyar ta buƙaci Gwamnatin Jihar Sokoto da hukumomin tsaro su gudanar da cikakken bincike ba tare da nuna son kai ba kan harin da aka kai wa Lukuwa da kuma zargin kashe wanda ake zargi da kai masa harin.

Ƙungiyar ta buƙaci shugabannin addinai, hukumomin gargajiya, ‘yan siyasa da sauran jama’a su yi haƙuri tare da kauce wa kalamai ko ayyukan da za su iya ƙara rura wutar rikicin addini.

Kara karanta wannan

Malam Murtala Bello ya faɗi shirinsu da aka kai wa Sheikh Lukuwa hari a Sokoto

Yan sandan Sokoto sun yi gargadi

Kun ji cewa Rundunar ‘Yan Sandan Sokoto ta ja hankalin al'ummar jihar bayan mummunan harin da aka kai kan Sheikh Musa Lukuwa.

Yan sanda sun yi kira ga jama’a su kwantar da hankula tare da guje wa ɗaukar fansa bayan harin da aka kai wa babban malamin addinin musulunci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262