Boye Boye Ya Kare, Amurka Ta Bayyana Gagarumar Barnar da Iran Ta Yi Mata
- Ofishin mai binciken cikin gida na Ma'aikatar Tsaron Amurka ya fitar da rahoto na farko kan asarar da aka yi a yaƙin Iran
- Haren-haren Iran sun lalata daruruwan gini da wuraren ajiyar sojojin Amurka a ƙasashe takwas na yankin Gabas Tsakiya
- Sojojin Amurka sun fuskanci ƙalubale mai tsanani sakamakon lalacewar sansanoninsu da kuma ƙarewar makaman kariya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Washington – Ofishin mai binciken cikin gida na Ma'aikatar Tsaron Amurka (Pentagon) ya fitar da wani rahoto na gaggawa game da yaƙin Iran, wanda shi ne na farko a hukumance da ya keɓance asarar kayan aiki da gine-ginen sojin Amurka.
Kamar yadda rahoton ya bayyana ta hanyar amfani da bayanan da aka samu daga rundunar sojin Amurka ta CENTCOM, harhare-haren Iran sun lalata daruruwan gine-gine da wuraren ajiyar sojojin Amurka.

Source: Getty Images
Tashar labarai ta CNN ta ruwaito cewa rahoton da ya ƙunshi lokacin da aka fara yaƙin daga ranar 28 ga Fabrairu zuwa 30 ga Yuni, ya tabbatar da irin matsalar da aka fuskanta saboda ƙarewar makaman kariya.
Haka zalika rahoton ya bayyana cewa harin ya shafi ƙasashe irin su Kuwait, Bahrain, Qatar, UAE, Saudi Arabia, Iraq, Oman da kuma Jordan da Amurka ke ajiye sojoji.
Matakan da Amurka ta ɗauka
A cewar rahoton, haren-haren Iran sun haifar da gagarumin canji game da yadda dakarun Amurka suke gudanar da ayyukansu a yankin, inda ma'aikatar tsaron ta karkata da kuma canza wuraren ajiyar kayayyaki da mutanenta.
Ya rubuta cewa:
"Lalacewar babbar cibiyar rundunar sojin ruwa a Bahrain, wadda mukaddashin shugaban rundunar sojin ruwa Hung Cao ya ce 'Iran ta cinna mata wuta sosai', ta ƙara rura wutar ƙalubale tare da tilasta maido da cibiyar zuwa tsibirin Diego Garcia mai nisa."
Asarar cibiyoyin jakadancin Amurka
Rahoton Groud News ya bayyana cewa hare-haren Iran da ƙawayenta sun haifar da lalacewar gine-ginen jakadancin Amurka wanda kudinsu ya kai kusan dalar Amurka miliyan 184.
A farkon watan Maris, jirage marasa matuka guda biyu na Iran sun kai hari kan ofishin jakadancin Amurka da ke Riyadh, inda suka janyo babbar lalacewa ciki har da ofishin hukumar leken asiri ta CIA.

Source: Getty Images
Ana sanya ran waɗannan canje-canje da aka samu a tsarin sojin Amurka a yankin za su ci gaba da kasancewa na dindindin har zuwa lokacin da za a kammala yaƙin.
Iran ta farmaki jirgin Amurka
A wani labarin daban, kun ji cewa rundunar tsaron juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta sanar da cewa ta lalata jirage marasa matuƙa biyu nau'in MQ-1 na Amurka a kusa da mashigar Hormuz.
Rundunar ta bayyana cewa an harbo jiragen ne gabashin hanyar ruwan ta hanyar amfani da sabon tsarin kariya na sojin sararin samaniyar ƙasar.
Wannan mataki ya biyo bayan rikicin da ya barke tsakanin ƙasashen biyu game da tsaron hanyoyin ruwa da kasuwanci a yankin mashigar Hormuz.
Asali: Legit.ng

