Bayan Abin da Ya Faru, Gwamnatin Sakkwato Ta Rufe Masallacin Sheikh Musa Lukuwa

Bayan Abin da Ya Faru, Gwamnatin Sakkwato Ta Rufe Masallacin Sheikh Musa Lukuwa

  • Gwamnatin Jihar Sokoto ta bayar da umarnin rufe Masallacin Juma’a na Sheikh Musa Lukuwa da ke Mabera bayan harin da ya yi sanadin kisa
  • Gwamnatin ta kafa kwamitin malaman addinin Musulunci domin binciken musabbabin rikicin da kuma hanyoyin hana sake faruwar lamarin
  • An bayyana masallacin a matsayin wurin da aka aikata laifi, kuma zai ci gaba da kasancewa a rufe har sai an ba da wani sabon umarni

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto, Nigeria - Gwamnatin Jihar Sokoto ta bayar da umarnin rufe Masallacin Juma’a na Sheikh Musa Lukuwa da ke Mabera, cikin birnin Sokoto, bayan abin da ya faru a masallacinnwanda ya yi sanadin kisa.

Gwamnatin ta kuma kafa wani kwamiti na malaman addinin Musulunci domin binciken musabbabin lamarin na kusa da na nesa, tare da ba ta shawarar matakan da suka dace domin hana sake faruwar irin wannan abu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Anambra ta fallasa Peter Obi ana tsakar takarar shugaban kasa

Gwamna Ahmed Aliyu.
Gwamnan jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu a wurin kaddamar da rabon tallafin abinci ga mabukata Hoto: Ahmed Aliyu Sokoto
Source: Facebook

Dalilin rufe masallacin Sheikh Lukuwa

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Gidan Gwamnatin Sokoto, Abubakar Bawa, ya fitar ranar Talata.

Ya ce masallacin da gwamnati ta bayyana a matsayin wurin da aka aikata laifi zai ci gaba da kasancewa a rufe har sai an ba da wani sabon umarni.

Matakin ya biyo bayan tashe-tashen hankulan addini da aka samu a wasu sassan birnin Sokoto, ciki har da rahoton daba wa wani malamin addinin Musulunci, Malam Musa Lukuwa, wuka jim kadan bayan ya jagoranci sallar Juma’a a masallacin.

Gwamnati ta kafa kwamitin bincike

Gwamnatin ta ce kwamitin zai binciki abubuwan da suka jawo tashin hankalin tare da gabatar da shawarwari domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

Haka kuma, ta bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan harin da kuma kisan da ya biyo baya a masallacin.

Kara karanta wannan

Duk da sace malamai maza, malaman addini mata sun goyi bayan Tinubu

Gwamnatin Sakkwato ta kuma nisanta kanta daga duk wani mutum, ba tare da la’akari da matsayinsa ba, da ke fakewa da addini domin zagon kasa ko nuna rashin girmamawa ga Annabi Muhammad (SAW), iyayensa, iyalansa da sahabbansa.

Musa Lukuwa.
Babban malamin addinin musulunci a Sakkwato, Sheikh Musa Lukuwa Hoto: Sahalu Musa Lukuwa
Source: Facebook

Gwamnatin Sakkwato ta dauki matsaya

Ta sake tabbatar da “cikakkiyar biyayya da girmamawa” ga Annabi, iyayensa, iyalansa da sahabbansa, tare da kira ga mazauna jihar da su ci gaba da nuna masa kauna da tausayi.

Gwamnatin ta roki mazauna jihar da su guji yin kalaman tunzura jama’a da ka iya kawo cikas ga zaman tare cikin lumana da Sokoto ta shahara da shi.

Ta kuma tabbatar wa mazauna jihar cewa ta kuduri aniyar kare rayuka da dukiyoyin kowane dan kasa a jihar.

MURIC ta yi Allahi wadai da lamarin

A wanai labarin, kun ji cewa ƙungiyar MURIC ta yi Allah wadai da harin da aka kai wa Sheikh Musa Lukuwa da kuma zargin kashe wanda ake zargi da kai harin.

MURIC ta kuma soki hukumomin tsaro da na gwamnati bisa zargin gaza ɗaukar matakan da suka dace tun da wuri kan abin da ta bayyana a matsayin kalamai masu kawo cece-ku-ce da malamin ya riƙa yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262