Zargin Ta’addanci: Sanata Buba Ya Shiga Kotu da Matashi da Ya Yi Tone Tone

Zargin Ta’addanci: Sanata Buba Ya Shiga Kotu da Matashi da Ya Yi Tone Tone

  • Sanata Shehu Buba Umar ya bukaci hukumomi su gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake masa na alaƙa da ’yan ta’adda
  • Sanatan ya kalubalanci Hassan da ya gabatar da duk wata hujja da yake da ita ga hukumomin tsaro domin gudanar da bincike na doka
  • Masu goyon bayan Shehu Buba sun ce ba za su amince da amfani da kafafen sada zumunta wajen yada zarge-zargen da ba a tabbatar ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja — Sanata Shehu Buba Umar ya bukaci a dauki matakin doka kan zarge-zargen da ake danganta shi da ayyukan ’yan ta’adda.

Sanatan ya kuma kalubalanci wanda ya yi zargin, Hassan, da ya gabatar da hujjojin da yake da su ga hukumomin da suka dace.

Sanata Buba ya yi korafi kan zargin alakanta shi da ta'addanci
Sanata Shehu Buba daga Bauchi da ake zargin yana da alaka da ta'addanci. Hoto: Mujaddadi TV.
Source: Facebook

Hakan na cikin wasu takardun korafi da sanatan ya fitar wanda shafin yada manufofinsa, Mujaddadi TV ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Kamfanin Opay ya nemi agajin DSS, ƴan sanda kan jita jitar zai gudu a Najeriya

Matsayar sanatan kan zarginsa da ake yi

Matsayar sanatan ta biyo bayan yaduwar wasu bidiyoyi da ake zargin suna da alaƙa da shi, da kuma ikirarin Hassan.

Hassan ya yi ikirarin cewa Shehu Buba na da alaƙa da ’yan ta’adda, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a.

A cewar wata sanarwa da magoya bayan sanatan suka fitar, an gabatar da korafe-korafe kan zarge-zargen da bidiyoyin ga hukumomin tsaro tun shekarar 2025.

Sanarwar ta ce Hassan, wanda ke ci gaba da yin zarge-zargen ta kafafen yaɗa labarai, bai bayyana gaban hukumomin tsaro ba.

An ce hakan ya faru ne duk da cewa rahotanni sun nuna an gayyace shi domin ya gabatar da hujjojin da yake da su.

Saboda haka, sanatan da magoya bayansa sun bukaci hukumomin da suka dace su binciki zarge-zargen tare da daukar matakin doka.

Sanarwar ta ce: “Ba mu da wata matsala da bincike ko tambayoyi daga hukumomin da suka dace.”

Kara karanta wannan

Nafiu Bala ya kawo sabon rikici a ADC kan yadda Atiku ke sukar Tinubu

Ta kuma jaddada cewa duk wanda yake da sahihiyar hujja kan sanatan ya kamata ya gabatar da ita a hukumomin tsaro.

Masu goyon bayan sanatan sun ce bai kamata a gudanar da zarge-zarge masu tsanani irin wadannan ta kafafen sada zumunta ba.

Sun ce ya kamata a bi hanyoyin doka da binciken hukumomi da aka tanada domin tabbatar da gaskiyar zarge-zargen.

Sanata Buba ya kalubalanci matashi Hassan kan zargin ta'addanci
Sanata Shehu Buba da matashi Hassan da ke tone-tone a kansa. Hoto: Mujaddadi TV.
Source: Facebook

Zargin da Shehu Buba ke yi wa Hassan

Sanarwar ta kuma zargi Hassan da kokarin lalata mutuncin sanatan ta hanyar abin da ta bayyana a matsayin zarge-zargen alaka da ta'addanci.

Sanarwar ta bukaci Hassan ya gabatar da duk wata hujja da yake da ita ga hukumomin da suka dace domin gudanar da bincike.

Ta ce bincike na hukuma zai samar da damar tantance zarge-zargen cikin gaskiya da kuma ba tare da son zuciya ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa:

“Ba za mu amince da amfani da zarge-zargen da ba su da tushe, ɓata suna ko yada bayanan da ba a tabbatar ba a matsayin kayan siyasa ba.”

Ta ce ba za a yi amfani da irin wadannan zarge-zarge wajen bata sunan wani mutum saboda dalilan siyasa ba.

Kara karanta wannan

Gwamna ya hana ayyukan 'Hisbah' a jiharsa, ya ba jami'an tsaro umarni

MURIC ta kare Sanata Shehu Buba

An ji cewa Kungiyar MURIC ta yi Allah wadai da zargin Sanata Shehu Buba da ake yi da ɗaukar nauyin ta'addanci a Najeriya.

Kungiyar kare hakkin Musulmai ta ce babu hujjoji kan zargin sanatan wanda ya kasance haziki da ke hidimtawa al'ummarsa.

Hakan ya biyo bayan zargin da gwamnatin jihar Bauchi ta yi kan sanatan da daukar nauyin dan ta'adda zuwa aikin hajji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.