Allah Ya Kawo Mu, Sarkin Musulmi Ya Fitar da Sanarwa kan Ranar Babbar Sallah a Najeriya
- Sarkin Musulmi a Najeriya ya bukaci a fita duban jinjirin watan Zul-Hijja na shekarar 1447AH, watan da Musulmai ke gudanar da idin layya
- A wata sanarwa da fadar Sarkin Musulmi ta fitar, ta ce za a fara duban watan ne a gobe Lahadi, 17 ga watan Mayu, 2026
- A ranar 10 ga watan Zul-Hijja ne musulmai a fadin duniya ke gudanar da babbar Sallah, kwana daya bayan hawan Arafah
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Sokoto, Nigeria - Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya bukaci daukacin al'ummar musulmin Najeriya su fita duban jinjirin watan Zul-Hijja, 1447AH.
Sarkin Musulmi, wanda shi ne Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA) ya bukaci a fara duban jinjirin watan daga gobe Lahadi, 29 ga watan Zul Ki'ida, 1447 daidai da 17 ga watan Mayu, 2026.

Source: Getty Images
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da shafin masarautar Sarkin Musulmi da ke Sakkwato, Daular Usmaniyya, ya wallafa a Facebook yau Asabar, 16 ga Mayu, 2026.
Za a fara duban watan Sallah a Najeriya
Sanarwar na dauke da sa hannun shugaban kwamitin ba da shawarwari kan harkokin addinin musulunci na masarautar Sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Walo Junaidu (Wazirin Sakkwato).
Samarwar ta ce:
"Ana sanar da al’ummar Musulmi cewa ranar Lahadi 17 ga Mayu, 2026, wadda ta yi daidai da ranar 29 ga watan Zul-ki’ida 1447AH, ita ce ranar duban jinjirin watan Zul-Hijja 1447AH.
"Don haka ana roƙon Musulmi da su fara neman ganin jinjirin watan Zul-hijja 1447AH a ranar Lahadi.
"Sannan duk wanda ya ga watan ya kai rahoto ga Hakimai ko dagattai mafi kusa da shi domin isar da sakon ga Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar CFR, mni, Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA)
Sanarwar ta kuma yi addu'ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya taimaka domin sauke wannan nauyin na addini.

Source: Twitter
Yaushe za a yi babbar Sallah?
Bisa wannan sanarwa, Legit Hausa ta fahimci cewa idan an ga wata a gobe Lahadi, ranar Litinin, 18 ga watan Mayu, 2026 zai zama ranar 1 ga watan Zul-hijja, sannan babbar Sallah za ta kama ranar Laraba, 27 ga watan Mayu.
Amma idan watan ya buya ba a samu ganinsa ba, watan Zul-Hajji zai shiga a ranar Talata, 19 ga watan Mayu, 2026, sannan za a yi babbar Sallah ranar Alhamis, 28 ga Mayu.
An bada hutun babbar Sallah a Turkiyya
A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Recep Erdoğan ya ba da sanarwar ƙara hutun Sallar Layya na shekarar 2026 zuwa kwanaki tara ga ma'aikatan gwamnati a Turkiyya
Ma'aikata a Turkiyya za su fara hutunsu ne daga ranar Talata, 26 ga watan Mayu da rana, inda aka ba su ƙarin kwana ɗaya da yini na hutun kafin ranar Idi.
Sallar layya, wadda Turkawa ke kira da Kurban Bayram, tana ɗaya daga cikin manyan bukukuwan Musulunci da ake gudanarwa a kasar.
Asali: Legit.ng

