Tattalin Arziki: Yadda Najeriya Tayi Asarar Naira Tiriliyan 20 a Yunkurin Canza Kudi

Tattalin Arziki: Yadda Najeriya Tayi Asarar Naira Tiriliyan 20 a Yunkurin Canza Kudi

  • Abin da mutane suka rasa daga lokacin da aka canza kudi zuwa yau, ya kai Naira Tiriliyan 20
  • Shugaban CPPE ya yi Allah-wadai da yadda aka yi kokarin canza takardun N200, N500 da N1000
  • Muda Yusuf ya ce tattalin arziki ya ruguje kuma jama’a sun rasa abin yi a dalilin tsarin na CBN

Abuja - Ana lissafin tattalin arzikin kasar nan ya rasa kusan Naira Tiriliyan 20 a sakamakon karancin kudi wanda hakan ya jawo harkoki suka tsaya.

Wani rahoto da aka fitar a Tribune ya nuna canjin kudi ya taba kasuwanci, harkar noma, kananan saye-da-sayarwa da musamman khada-hada a kauyuka.

CPPE mai kokarin jawo ‘yan kasuwa masu zaman kansu ta ce tsarin da aka yi kokarin fito da shi ya yi sanadiyyar da dubu daruruwa suka rasa ayyukan yi.

Kara karanta wannan

“Kudi Da Nake Nema” Matashi Ya Yi Bidiyon Buhuhunan Tsoffin Kudi Da CBN Ya Nika Ya Watsar

A wani jawabi na musamman da cibiyar ta fitar, tayi kira da babban murya ga shugaba Muhammadu Buhari da CBN a kawo karshen karancin kudi.

Mutane su na wayyo Allah

Kamar yadda rahoto ya zo Nigerian Tribune, cibiyar ta koka cewa baya ga karya tattalin arziki da canza kudi ya jawo, ta kai mutane sun shiga halin kunci.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Darektan CPPE a Najeriya, Dr. Muda Yusuf ya ce Naira Tiriliyan 20 ake kintacen an rasa, abin da ya haddasa wannan shi ne canza N200, N500 da N1000.

Buhari
Buhari zai koma Abuja Hoto: @BuhariSallauOnline
Asali: Facebook

A cewar Dr. Muda Yusuf, ba ayi tunani da kyau wajen canjin takardun kudi da ya kawo masifa ba. The Cable ta kawo labarin nan a farkon makon nan.

La’akari da cewa bankin CBN ya janye fiye da 70% na kudin da ke yawo a cikin al’umma, miliyoyin ‘yan Najeriya sun kara burmawa talauci da fatara.

Kara karanta wannan

Sauya Naira: Manyan Arewa Sun Fada Wa Shugaba Buhari Abinda Zai Faru Idan Ya Ki Bin Umarnin Kotun Koli

A lokacin da aka fitar da jawabin, shugaban na CPPE ya yi Allah-wadai da yadda bankin CBN ya yi gum bayan kotun koli ta hallata amfani da tsohon kudi.

Ana haka ne sai ga rahoto cewa gwamnan babban anki ya yi biyayya ga kotun koli, ya umarci bankuna su koma karba da kuma bada tsofaffin Nairorin.

A karshen jawabinsa, Yusuf ya bukaci Mai girma Shugaba Muhammadu Buhari ya fito gaban kowa, ya ba ‘Yan Najeriya hakuri kan halin da aka jefa su.

Tinubu ya tuna Yarbawa - Fayose

Ganin Jam’iyyar APC ta lashe zabe, an ji labari jigo a PDP, Ayodele Fayose ya jerowa Bola Tinubu abin da Yarbawa suke nema idan ya shiga fadar Aso Rock.

Tsohon gwamnan Ekiti yana so Tinubu ya zama Shugaban kowane Bayarabe a kasar nan ba illa na APC ba, ya ce kyau a rika tunawa da yarbawa a mukamai

Kara karanta wannan

Sabbin Naira: Masani ya fadi kura-kurai 5 da CBN ya yi wajen kawo batun sauyin Naira

Asali: Legit.ng

Online view pixel