Najeriya Ta Yi Rashi: Babban Malamin Addinin Musulunci Ya Rasu
- Al’ummar Musulmin Najeriya a Ireland sun sanar da rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci wanda ya koma ga Mahaliccinsa
- Marigayin ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa da bunƙasa ƙungiyoyin Musulmin Najeriya a wasu sassan Ireland
- An gudanar da Sallar Jana’izar sa a Masallacin IFI Dublin ranar Juma’a, 11 ga Satumba, 2026, sannan aka binne shi a makabartar Musulmi ta Drogheda
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Dublin, Ireland - Al’ummar Musulmin Najeriya da ke Ireland sun sanar da rasuwar Imam Abdul-Ganiy Adeleke Asubiaro, wanda aka fi sani da Alfa Gani, fitaccen malamin addinin Musulunci kuma jagoran al’umma.
Al’ummar ta bayyana marigayin a matsayin ɗaya daga cikin mutanen da suka taka muhimmiyar rawa wajen kafa da bunƙasa tsarin rayuwar Musulmin Najeriya a Ireland.

Source: Facebook
A cikin wata sanarwa da al’ummar ta fitar ranar Lahadi, 6 ga Satumba, an bayyana Alfa Gani a matsayin ɗaya daga cikin jiga-jigan farko da suka taimaka wajen haɓaka rayuwar Musulmin Najeriya a ƙasar.
Alfa Gani ya taka rawa wajen sasanta rikice-rikice
Mutanen da suka san marigayin sun bayyana shi a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda suka fara jagorantar al’ummar Musulmin Najeriya a Ireland.
An ce ya taka rawa wajen tallafa wa kafa da bunƙasa ƙungiyoyin Musulunci a ƙananan hukumomi da yankuna daban-daban na Ireland.
Ya kuma yi fice wajen shirya karatun tafsirin Ramadan na iyalai da yake gudanarwa duk shekara, inda yake magana kan matsalolin da iyalai Musulmi ke fuskanta.
A cikin wa’azinsa, ya kan ƙarfafa iyaye su rungumi tarbiyya mai kyau da ta dace da koyarwar Musulunci, tare da la’akari da ƙalubalen rayuwar zamani.
Bayan aikin ilimi da wa’azi, waɗanda suka san shi sun ce Alfa Gani mutum ne mai haɗa kan jama’a, mai natsuwa kuma wanda mutane suka yarda da shi wajen sasanta rikice-rikice.
An ce sau da dama ana kiransa domin taimakawa wajen sasanta matsalolin iyalai da kuma saɓani tsakanin ƙungiyoyin al’umma.
Sun kuma bayyana shi a matsayin mutum mai faɗin gaskiya da magana kai tsaye idan yanayi ya buƙaci hakan.
An yi jana’izar Alfa Gani a Ireland
Al’ummar Musulmin Najeriya da ke Ireland ta bayyana matuƙar jimami kan rasuwar malamin, tana mai yabawa da irin gudunmawar da ya bayar wajen jagoranci, nasiha da shiryar da al’umma tsawon shekaru.
Ƙungiyoyin Musulunci da mambobin al’umma sun yi addu’o’in neman gafara ga marigayin, tare da roƙon Allah Ya yafe masa kura-kuransa, Ya sanya shi cikin Aljannatul Firdausi.
Haka kuma, sun roƙi Allah Ya ba iyalansa ƙarfin hali da haƙurin jure rashin ɗansu, ɗan’uwansu, da mahaifinsu.
Bayan rasuwarsa, Islamic Foundation of Ireland (IFI) ce ta jagoranci shirye-shiryen binne shi. An miƙa gawarsa domin gudanar da wanka bisa tsarin Musulunci, sannan aka gudanar da Sallar Jana’iza a Masallacin IFI Dublin ranar Juma’a, 11 ga Satumba, 2026.
Daga nan aka kai shi Makabartar Musulmi ta Drogheda, inda aka yi masa jana’iza.

Source: Facebook
Tsohon shugaban PDP na kasa ya rasu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban Jam’iyyar PDP na ƙasa, Bamanga Muhammad Tukur, ya rasu yana da shekara 91.
Marigayin ya rasu ne bayan ya shafe wani lokaci yana fama da rashin lafiya, inda rsuwarsa ta kawo ƙarshen rayuwar wani fitaccen ɗan siyasa da ɗan kasuwa.
Asali: Legit.ng

