Akwai Kura: Hare Haren Jirage Marasa Matuka Sun Jawo Gagarumar Matsala a Saudiyya
- Saudiyya ta rufe bututun mai na East-West mai tsawon kilomita 1,200 a matsayin matakin kariya bayan harin jirage marasa matuka daga Iraq
- Iraq ta tabbatar da cewa an harba jiragen daga jihar Maysan da ke iyaka da Iran, tare da ƙaddamar da bincike kan harin
- Mayakan Houthi sun ce sun mallaki mashigar Bab al-Mandab, lamarin da ya ƙara matsin lamba kan jigilar kayayyaki da farashin ɗanyen mai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Riyadh, Saudiyya - Saudiyya ta rufe wani muhimmin bututun mai bayan an kai masa hari da jirage marasa matuka da aka harba daga Iraq.
Rufe bututun na zuwa ne yayin da faɗa a Gabas ta Tsakiya ke ƙara yin barazana ga muhimman ababen more rayuwa na makamashi da hanyoyin jigilar kayayyaki.

Source: Getty Images
A cewar BBC, bututun East-West, wanda ya kai tsawon kilomita 1,200, yana bai wa Saudiyya damar fitar da mai ba tare da dogaro da mashigar Hormuz ba.

Kara karanta wannan
Duk da Najeriya ta yi ƙokari, yaƙin Amurka da ƙasar Iran ya haifar da babbar asara a duniya
An rufe bututun ne a matsayin matakin kariya ranar Juma’a, 11 ga watan Satumban 2026 bayan harin da aka kai.
An samu raunuka da lalacewar abubuwa
Ma’aikatar Harkokin Wajen Saudiyya ta ce harin ya jikkata wasu mutane tare da haddasa lalacewar abubuwa. Sai dai ta ce ana ci gaba da tantance girman barnar da harin ya haifar.
A nata bangaren, gwamnatin Iraq ta tabbatar da cewa an harba jirage marasa matuka daga jihar Maysan, wadda ke kan iyaka da Iran.
Aljazeera ta ruwaito cewa hukumomin Iraq sun kuma cire wani kwamandan soja daga mukaminsa tare da ƙaddamar da bincike kan lamarin.
Saudiyya ta ƙi mayar da martani
Saudiyya ba ta kai wani hari na ramuwar gayya ba bayan harin. Ma’aikatar Harkokin Wajen ƙasar ta ce matakin ya biyo bayan kiran da Firaministan Iraq ya yi.
Saudiyya ta ce za ta “tallafa wa ƙoƙarin gwamnatin Iraq” wajen “hana hare-haren” da ake ƙaddamarwa daga ƙasar zuwa makwabtan ƙasashe.
Bututun na ɗaukar kaso mai yawa na man duniya
A cewar Reuters, wadda ta nakalto kamfanonin bin diddigin jiragen ruwa da masu nazarin harkokin mai, bututun East-West ya kasance yana jigilar kusan kashi 4 zuwa 5 cikin 100 na man da ake samarwa a duniya.
Muhimmancin bututun ya ta'allaka ne kan yadda yake bai wa Saudiyya damar kauce wa mashigar Hormuz wajen jigilar man fetur.
Saboda haka, rufe shi na iya ƙara matsin lamba kan hanyoyin samar da makamashi a yankin.
Houthis sun ce sun mallaki Bab al-Mandab
Harin ya zo ne a daidai lokacin da mayakan Houthi da Iran ke mara wa baya ke ci gaba da samun ƙarfi a Yemen.
Houthis sun ƙwace iko da wani babban ɓangare na gabar tekun ƙasar. Kungiyar ta kuma yi ikirarin cewa ta mallaki mashigar Bab al-Mandab, wadda muhimmiyar hanyar ruwa ce da ta haɗa Bahar Maliya da mashigar Suez.
Sai dai Houthis sun ce zirga-zirgar jiragen ruwa za ta ci gaba da kasancewa cikin aminci ga dukkan kamfanoni, ban da jiragen ruwan Saudiyya.

Source: Getty Images
Yariman Saudiyya ya roki Trump
A wani labarin kuma, kun ji cewa Yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman (MBS), ya kira Shugaban Amurka Donald Trump.
Mohammed bin Salman ya roƙi Shugaba Trump da ya umarci sojojin Amurka su kai hare-hare kan mayakan Houthi na kasar Yemen.
Asali: Legit.ng

