An Kama Tsohuwa da Makamai, ana Zargin za Ta kai wa 'Yan Bindiga

An Kama Tsohuwa da Makamai, ana Zargin za Ta kai wa 'Yan Bindiga

  • Sojojin Operation Fansan Yamma sun kama wani da ake zargi da jagorantar ’yan ta’adda da wasu mambobin ƙungiyarsa a Kaduna
  • Haka kuma, an kama wata mata mai akalla shekara 50 da ake zargi da safarar alburusai 300 zuwa hannun ’yan ta’adda
  • Sojojin sun kuma kama wani da ake zargi da samar da kayan aiki ga ’yan ta’adda, inda aka kwato wayoyin sadarwa guda hudu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation Fansan Yamma, sun kama wasu mutane da ake zargi da hannu wajen ayyukan ta’addanci a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun bi masu garkuwa har cikin daji sun masu jina jina

An gudanar da samamen ne ranar Laraba, 9 ga Satumba 2026, a ƙananan hukumomin Kubau, Igabi da Birnin Gwari.

Matar da aka kama a Kaduna
Matar da ake zargi da safarar makami a Kaduna. Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

Zagazola Makama ya wallafa a X cewa an kai hare-haren ne kan maboyar ’yan ta’adda, hanyoyin safarar kayayyaki da kuma hanyoyin da ake amfani da su wajen tallafa wa ƙungiyoyin ta’addanci.

An kama shugaban ’yan ta’adda

Da sanyin safiyar Laraba, dakarun Najeriya sun gudanar da samame a Dabar Dabo, wata maboyar ’yan ta’adda da aka sani a ƙaramar hukumar Kubau.

A yayin samamen, sojojin sun kama wani da ake zargi da jagorantar ’yan ta’adda tare da wasu mambobin ƙungiyarsa guda biyu.

Rahotanni sun nuna cewa rundunar ta ce an tsare mutanen uku domin ci gaba da gudanar da bincike da tattara bayanan sirri.

An kama tsohuwa a Kaduna

A wani samame daban, sojoji sun kama wata mata mai shekaru 50 a ƙaramar hukumar Igabi bisa bayanan sirri kan safarar alburusai.

Ana zargin an kama matar ne dauke da alburusai 300 da aka ɓoye a cikin wata jaka.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun bindige babban manajan banki a Najeriya har ya mutu

Binciken farko ya nuna cewa matar ta yi tafiya daga jihar Zamfara zuwa Lafia, inda ake zargin ta karɓi alburusai domin kai su ga ’yan ta’adda da ke aiki a yankin Birnin Gwari na Kaduna.

Sojojin sun tsare matar tare da alburusan da aka kwato, yayin da ake ci gaba da bincike domin gano sauran mutanen da ke cikin hanyar sadarwar.

Taswirar jihar Kaduna
Taswirar jihar Kaduna. Hoto: Legit
Source: Original

An kama wani dan ta’adda

Daga bisani a wannan rana, dakarun Sector 1 tare da haɗin gwiwar ’yan sa-kai na al’umma sun kama wani mutum da ake zargi da samar da kayan aiki ga ’yan ta’adda a Birnin Gwari.

A yayin binciken farko da yi masa tambayoyi, sojojin sun kwato na’urorin sadarwa guda hudu da ake zargin an yi amfani da su wajen ayyukan ’yan ta’adda.

An kuma kai wanda ake zargin da na’urorin da aka kwato zuwa hannun sojoji domin ci gaba da bincike.

An ceto mutane a Kaduna

Kara karanta wannan

An cafke dan sandan bogi da ya shiga Kano ya rika damfarar jama'a

A wani labarin, mun ruwaito cewa Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta ceto wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su tare da kashe wasu mutane biyu da ake zargi da yin garkuwa da mutane.

Lamarin ya faru ne yayin wani samame da aka gudanar a ranar Talata, 8 ga Satumba, a yankin Auchanawa da Wambai da ke ƙaramar hukumar Ikara.

’Yan sandan sun ce sun yi musayar wuta da waɗanda ake zargin masu garkuwa da mutanen ne, inda suka shiga dajin tare da tarwatsa sansanin masu laifin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng