Duk da Najeriya Ta Yi Kokari, Yakin Amurka da Kasar Iran Ya Haifar da Babbar Asara a Duniya

Duk da Najeriya Ta Yi Kokari, Yakin Amurka da Kasar Iran Ya Haifar da Babbar Asara a Duniya

  • Hukumar IEA ta ce an yi asarar gangar mai kusan biliyan 2.8 da ake fitarwa ta Mashigar Hormuz tun bayan fara yaƙin Amurka da Iran
  • Ta ce wasu hanyoyin samar da mai, rage amfani da mai da kuma cire mai daga ma’ajiyar ƙasa sun cike babban ɓangaren gibin
  • Adadin man da ke ratsawa ta Mashigar Hormuz ya kai ganga miliyan 7.6 a kowace rana a watan Agusta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Hukumar Makamashi ta Duniya (IEA) ta kiyasta cewa an yi asarar gangar mai kusan biliyan 2.8 da ake fitarwa ta Mashigar Hormuz tun bayan fara yaƙin Amurka da Iran.

Sai dai IEA ta ce ƙarin samar da mai daga wasu wurare, amfani da mai daga ma’ajiyoyi da raguwar buƙatar mai sun cike babban ɓangaren gibin.

Danyen mai.
Gangunan danyen mai da ake hada hada a kasuwannin duniya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Leadershipr ta rahoti cewa hakan na kunshe ne a rahoton kasuwannin mai (OMR) na baya-bayan nan da hukumar da ke birnin Paris ta fitar.

Kara karanta wannan

Kaico: An tsinci gawar budurwa a wani yanayi bayan ta yi faɗa da saurayinta a Kaduna

Yadda yakik Iran ya jawo asara

Rahoton ya ce adadin man da ya ratsa Mashigar Hormuz ya kai ganga miliyan 7.6 a rana a watan Agusta, wato kusan ganga miliyan 13.1 a rana ƙasa da matakin da ake samu kafin yaƙin.

Hanyoyin fitar da mai da ke kauce wa Mashigar Hormuz sun rage asarar da rikicin ya haifar da fiye da ganga miliyan 500, wato matsakaicin ganga miliyan 2.8 a rana.

Jimillar fitar da mai daga Yanbu ta Saudi Arabia da Fujairah ta Hadaddiyar Daular Larabawa ta tashi daga ganga miliyan 4.1 a rana a watan Fabrairu zuwa miliyan 7.8 a kowace rana a watan Yuni.

Najeriya ta kara samar da mai

IEA ta ce ƙarin samar da mai daga ƙasashen da ke wajen yankin Tekun Mideast Hulf, ciki har da Amurka, Brazil, Kazakhstan, Venezuela da Najeriya, ya cike wani ƙarin gibin ganga miliyan 420 na asarar da aka tara.

Kara karanta wannan

'Ni na ci zaɓe a 2023': Kalaman Obi da suka dugunzuma fadar shugaban ƙasa

Ta ce sauran gibin da aka samu ya bayyana cewa an cike shi ne ta hanyar fito da mai daga ma’ajiyoyin ƙasa da kuma raguwar buƙata.

Kasashe sun fito da mai daga ma'ajiyoyi

IEA ta ce adadin man da ke cikin ma’ajiyar duniya ya ragu da sauri fiye da kowane lokaci, inda ya dawo ganga miliyan 507 ƙasa da matakin da aka samu kafin fara yaƙin.

Hukumar ta kiyasta cewa raguwar buƙatar mai a duniya tun bayan fara rikicin ta wuce ganga biliyan ɗaya, sakamakon gagarumar raguwar amfani da mai musamman a China da Gabas ta Tsakiya.

Ana sa ran samar da mai a duniya zai ragu da ganga miliyan 5.7 a rana a shekarar 2026 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, inda zai kai ganga miliyan 100.7 a rana.

Trump na duba yiwuwar karkare yakin

Kun ji cewa Shugaba Donald Trump ya yi hasashen cewa yaƙin da ake yi tsakanin Amurka da Iran zai ƙare nan take bayan zaɓen tsakiyar wa’adi na Nuwamba.

Trump ya bayyana haka ne yayin da kassshen biyu ke ci gaba da gwabza faɗa da ƙarin hare-hare kan jiragen ruwa a yankin, musamman a mashigar ruwa ta Hormuz.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262