Tsohon Gwamna Ya Faɗi dalilin Taimaka wa Obi da Aron Mota kafin a Jefe Shi
- Tsohon gwamnan Benue, Samuel Ortom, ya bayyana dalilin da ya sa ya bai wa Peter Obi motarsa yayin ziyararsa jihar Benue
- Ortom ya ce kin taimaka wa Obi zai zama rashin karimci, yana mai cewa Obi tsohon gwamna ne kuma babban jigo a siyasar Najeriya
- Ya kuma musanta zargin Hyacinth Alia cewa yana aiki da Obi, yana mai cewa ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu a 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Makurdi, Benue - Tsohon gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya bayyana dalilin da ya sa ya samar wa ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, da motarsa.
Ortom ya bayyana haka ne yayin da ake alakanta shi da abin da ya faru lokacin ziyararsa jihar a ranar Talata.

Source: Facebook
Ortom, wanda ya yi magana ta bakin mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Terver Akase, ya ce zai zama rashin dattako idan ya ƙi taimaka wa Obi da motarsa yayin ziyarar.
Ortom ya mayar da martani ne kan zargin Gwamnan Benue, Hyacinth Alia, cewa shi ne ya shirya ziyarar Obi zuwa jihar.
Ya ce:
“Ni ɗan siyasa ne mai fahimtar buƙatun hidimar jama’a da nauyin da ke tattare da jagoranci. Saboda haka, abin dariya ne da abin kunya a ce ana ƙoƙarin mayar da samar da mota ga wani ɗan Najeriya jagora laifi ko siyasa.
“Peter Obi tsohon gwamna ne, ɗan takarar shugaban ƙasa ne kuma ɗaya daga cikin fitattun ’yan siyasa a ƙasar. Ka yi tunanin yadda abin zai kasance idan Cif Ortom ya ƙi taimaka masa da sufuri yayin da yake Benue domin ziyarar jinƙai ga mutanen da suka rasa matsugunansu.
“Irin wannan ƙin taimako da ya yi zai kasance rashin dattako, rashin karɓar baƙi da kuma abin da bai dace da mutuncin tsohon gwamna ba. A haƙiƙa, ya kamata Gwamnatin Benue ta samar da irin wannan kulawa, kasancewar baƙon yana da babban matsayi."
Dangane da zargin cewa yana da “fuska biyu”, tsohon gwamnan ya bayyana zargin a matsayin “abin dariya”, yana mai cewa shi mutum ne mai cika alkawari kuma koyaushe zai tsaya kan ɗan takarar da ya bayyana goyon bayansa a bainar jama’a.
Ya ce a shekarar 2023, ya fito fili ya bayyana goyon bayansa ga Obi, amma yanzu ya bayyana goyon bayansa ga Shugaba Bola Tinubu.
Gwamna Hyacinth Alia da tsohon gwamnan Benue, Samuel Ortom, sun yi musayar kalamai kan ziyarar Peter Obi da ta gaza gudana a jihar.
Obi ya ziyarci Makurdi a ranar Talatar da ta gabata, inda ya shirya zuwa Yelewata domin jajanta wa iyalan waɗanda aka kashe a kisan kiyashin Yuni 2025.
Kwankwaso ya magantu bayan hari kan Obi
An ji cewa Rabiu Kwankwaso ya yi Allah-wadai da tare ayarin Peter Obi yayin da yake kan hanyar zuwa Benue, yana bayyana lamarin a matsayin barazana ga dimokuraɗiyya.
Tsohon gwamnan na Kano ya bukaci gwamnatin Benue ta tabbatar da tsaron Obi da tawagarsa, tare da ba su damar gudanar da zirga-zirga cikin ’yanci.
Masu zanga-zanga sun tare hanyar Gboko a Makurdi, suna rera “Ba ma son Peter Obi,” lamarin da ya hana ayarinsa ci gaba da tafiya.
Asali: Legit.ng

