'Kashe Kashe Ya Yi Yawa': An Taso Gwamna a Gaba Sai Ya Bar Kujerarsa
- Kungiyar HURIWA ta bukaci gwamna ya yi murabus bisa zargin gazawar gwamnatinsa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jiharsa
- Kungiyar ta ce an kashe mutane 11, ciki har da jami’an ’yan sandan tafi-da-gidanka guda hudu, yayin sabon hari a Ayilamo
- HURIWA ta kuma roki Shugaba Bola Tinubu ya karfafa ayyukan tsaro a Benue, tare da cafke wadanda suka kai hare-haren da masu daukar nauyinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja — Kungiyar Marubutan Kare Hakkin Bil’adama ta Najeriya, HURIWA, ta bukaci Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya yi murabus.
HURIWA ta dauki wannan matakin ne bisa abin da ta bayyana a matsayin gazawar gwamnatin Alia wajen kare rayuka da dukiyoyi.

Source: Twitter
A cikin wata sanarwa da Kodinetan Kasa na HURIWA, Emmanuel Nnadozie Onwubiko, ya fitar, kungiyar ta ce harin ya kara nuna muni, cewar Punch.

Kara karanta wannan
Ana cikin wahala a ƙasa, Atiku, Tinubu sun kwashi miliyoyin dala sun kashe a Amurka
Dalilin kiran Gwamna Alia ya yi murabus
Kungiyar ta ce hare-hare da kisan mutane na ci gaba da addabar jihar, lamarin da ke nuna tabarbarewar tsaro a Benue.
Bukatar HURIWA ta biyo bayan sabon hari da aka kai a garin Ayilamo da ke Tombo Ward, karamar hukumar Logo.
A yayin harin, an kashe mutane 11, ciki har da jami’an ’yan sandan tafi-da-gidanka guda hudu, kamar yadda ‘yan sanda suka tabbatar.
HURIWA ta ce:
“Gwamna Alia ba zai ci gaba da mulki kamar yadda zubar da jini a Benue wani kalubalen tsaro ne na yau da kullum ba.”

Source: Original
Hare-haren da yan bindiga ke kaiwa
Kungiyar ta bukaci gwamnan da ya “amince da alhakin gazawar gwamnatinsa wajen tsaro, sannan ya yi murabus idan ba zai iya tabbatar da kariyar mutanen da aka damka wa gwamnatinsa ba.”
Harin Ayilamo ya faru ne tsakanin daren Alhamis, 10 ga Satumba, zuwa safiyar Juma’a, 11 ga Satumba, lokacin da ‘yan bindiga suka mamaye garin.
‘Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutane 11, wadanda suka hada da fararen hula bakwai da jami’an ’yan sandan tafi-da-gidanka hudu.
An bayyana sunayen jami’an da aka kashe a matsayin ASP Paul Ina da Sufeto Mohammed Yusuf, Sufeto Oge Ikechukwu da Sufeto Edeh Andrew.
HURIWA ta yi Allah-wadai da harin, tare da bukatar hukumomin tsaro su gudanar da cikakken bincike domin gano tare da cafke wadanda suka kai harin.
Kungiyar ta kuma bukaci a gurfanar da wadanda aka kama a gaban kotu domin fuskantar hukunci bisa laifukan da ake zarginsu da aikatawa.
A cewar alkaluman, an kashe akalla mutane 6,896 a Benue tsakanin 29 ga Mayu, 2023, zuwa Mayu 2025, cewar Vanguard.
Peter Obi: Tsohon gwamna ya kare kansa
An ji cewa tsohon gwamnan Benue, Samuel Ortom, ya bayyana dalilin da ya sa ya bai wa Peter Obi motarsa yayin ziyararsa jihar Benue.
Ortom ya ce kin taimaka wa Obi zai zama rashin karimci, yana mai cewa Obi tsohon gwamna ne kuma babban jigo a siyasar Najeriya.
Ya kuma musanta zargin Hyacinth Alia cewa yana aiki da Obi, yana mai cewa ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu a 2027.
Asali: Legit.ng
