Matar Aure Ta Ce Ta Kama Mijinta Ya Yi Tsirara Yana Wanka da Wata Mata a Gidansu

Matar Aure Ta Ce Ta Kama Mijinta Ya Yi Tsirara Yana Wanka da Wata Mata a Gidansu

  • Wata mata mai suna Stella Mwalubanga ta kai mijinta, Elijah Mushayabanu, kotu bisa zargin ya fara yin nesa da ita bayan ta daina aiki saboda juna biyu
  • Stella ta ce matsalolin aurensu sun ƙara tsananta ne bayan ta koma gidan iyayenta domin samun kulawa yayin da take murmurewa daga tiyatar haihuwa
  • Ta kuma zargi mijinta da yin wanka da wata mace a gidansu tare da yawan kawo mata daban-daban, lamarin da ya sa ta nemi kotu ta raba aurensu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Zambia – Wata mata mai suna Stella Mwalubanga, mai shekaru 29, ta shaida wa Kotun Chelstone da ke Lusaka a Zambia cewa mijinta ya ce “aure yaudara ne” bayan ta tunkare shi kan zargin yin wanka da wata mace a gidansu.

Kara karanta wannan

Karin kudin fetur babu makawa yayin da ake wayyo lita ta haura N1300

Stella ta ce ta kai mijinta, Elijah Mushayabanu, mai shekaru 32, kotu domin neman a raba aurensu saboda matsalolin da suka addabi zamantakewarsu.

Wata mata ta yi karar mijinta a kotu
Sikeli da ke nuna alamar kotu. Hoto: Getty Images.
Source: Getty Images

Matsalolin aure sun fara tsananta

Rahoton da Tribune ta wallafa ya nuna cewa Stella ta ce ma’auratan sun yi aure a shekarar 2021 kuma suna da ’ya’ya uku.

Ta ce matsalolin sun fara tsananta ne bayan ta samu juna biyu da ɗansu na biyu kuma ta daina aiki a shekarar 2022.

A cewarta, mijinta wanda a baya yake nuna mata kulawa ya fara yin nesa da ita, yana kwana a wajen gida ba tare da bayani ba tare da nuna ƙarancin kulawa da halin da take ciki ba.

Batun wanka da wata mace

Stella ta ce Elijah ya furta kalaman nuna rashin kulawa ne bayan ta tunkare shi kan zargin yin wanka da wata mace yayin da take gidan iyayenta.

Ta kuma ce mijin ya gaya mata cewa yana zaman auren ne kawai saboda ya riga ya yi aure, kuma babu abin da zai iya yi a kai.

Kara karanta wannan

Matar Atiku ta shigo fage, Titi ta yi magana game da mulkin Shugaba Tinubu

Stella ta ƙara zargin cewa mijinta bai biya kuɗin aikin asibitin da aka yi mata ba, inda mahaifiyarta da ɗan’uwanta suka taimaka wajen biyan kuɗin.

Ta ce bayan ta koma gidan iyayenta, mijinta bai taɓa zuwa ganinta ba duk da ƙoƙarin da iyalansu suka yi na sasanta su.

Ƙoƙarin sulhu ya ci tura

Stella ta ce daga bisani iyalai biyu suka zaunar da ma’auratan domin tattaunawa, amma aka tambaye ta ko har yanzu tana son ci gaba da auren.

Ta ce ’yan uwan mijinta sun ba ta wata guda domin ta yanke shawara. Maimakon ta garzaya kotu, Stella ta ce ta koma gidan aurensu tare da roƙon mijinta ya kiyaye auren saboda ’ya’yansu.

Sai dai ta ce Elijah ya gaya mata cewa ba shi da ikon yanke hukunci kan lamarin, ya umurce ta da ta je wurin mahaifiyarsa da ke gona a Mpongwe domin ita ce za ta yanke hukunci.

Taswirar FCT Abuja
Taswirar FCT Abuja. Hoto: Legit
Source: Original

An kama mata da safarar makami

A wani labarin, mun ruwaito cewa sojojin Operation Fansan Yamma sun kama wasu da ake zargi da ayyukan ta’addanci tare da cafke wata mata ɗauke da harsasai a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

An shirya samar da kotu, gwamna zai kama yara a titi da ba su zuwa makaranta

Sojojin sun ce sun gudanar da ayyukan ne a ƙananan hukumomin Kubau, Igabi da Birnin Gwari a ranar 9 ga Satumba na shekarar 2026.

A wani samame, an kama wata mata mai shekaru 50 da ake zargi da ɗauke da harsasai 300 a cikin jaka, bayan ta yi tafiya daga Zamfara zuwa Lafia.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng