Yan Sanda 4 Sun Rasa Ransu bayan ’Yan Bindiga 200 Sun Kashe Wasu Mutane 8
- ‘Yan bindiga sun kashe jami’an ‘yan sandan MOPOL huɗu da mazauna Ayilamo takwas a wani mummunan hari da suka kai
- Wani mazaunin yankin ya ce sama da ‘yan bindiga 200 sun mamaye Ayilamo, inda suka yi harbe-harbe tare da kona gidaje a lokacin harin.
- Mazauna Ayilamo sun yi kira ga gwamnatin Benue da tarayya da su dauki matakan gaggawa domin kare rayuka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Makurdi, Benue - ‘Yan bindiga sun kashe jami’an ‘yan sandan tafi-da-gidanka, MOPOL, guda huɗu da mazauna Ayilamo takwas a gundumar Tombo, karamar hukumar Logo ta Benue.
Ayilamo wata al’ummar manoma ce da ke kan hanyar Abinsi-Tyulen-Anyiin-Wukari, kuma yankin ya sha fuskantar hare-haren ‘yan bindiga a lokuta daban-daban.

Source: Original
Yawan yan bindiga da suka shiga yankin
Wani mazaunin Ayilamo, Tyolumun Ugande, ya ce sama da ‘yan bindiga 200 dauke da makamai sun shigo yankin daga hanyar Alufu ta Taraba, suka nufi Ayilamo, cewar Punch.
Ugande ya ce ‘yan bindigar sun rika harbe-harbe tare da kona gidaje yayin da suke kutsawa cikin al’ummar, lamarin da ya haddasa fargaba tsakanin mazauna yankin.
Ya ce jami’an MOPOL da aka tura Ayilamo sun fuskanci ‘yan bindigar, wadanda ake zargin suna dauke da manyan makamai masu hatsari.
Ugande ya bayyana cewa bayan shafe sa’o’i ana musayar wuta, ‘yan bindigar sun ja da baya, amma an gano gawarwakin jami’an MOPOL huɗu a cikin jeji.
Ya ce an gano gawarwakin jami’an da safiyar Juma’a, bayan sun rasa rayukansu yayin da suke fafatawa da ‘yan bindigar da suka kai harin.
Ugande ya ce:
“Mun kuma gano gawarwakin mazauna Ayilamo takwas wadanda ‘yan bindigar suka kashe.
Jami’in ‘yan sanda mai kula da Ayilamo ya tabbatar da harin da kashe-kashen, inda ya ce:
“Mun nemi a kawo karin jami’ai.”

Source: Twitter
Yadda aka kashe yan sanda 4
Wani mazaunin yankin, James Udough, ya shaida wa The Nation cewa wannan sabon hari shi ne karo na biyu cikin wata guda da aka kashe jami’an MOPOL da aka tura Ayilamo.
Udough ya ce ‘yan bindigar sun shafe sama da shekaru biyu suna kokarin kona Ayilamo baki daya, lamarin da ya kara jefa mazauna cikin fargaba da rashin tsaro.
Ya ce:
“Yan bindigar sun shafe sama da shekaru biyu suna kokarin kona Ayilamo baki daya. Muna kira ga gwamnatin Benue da gwamnatin tarayya da su taimaka wajen kare kasarmu da rayukanmu.”
Yan bindiga sun sace fasinjoji 18 a Abuja
An ji cewa tsagerun yan bindiga sun yi garkuwa da fasinjoji 14 da ke tafiya daga Enugu zuwa babban birnin tarayya Abuja.
Rahotanni daga Rundunar ’Yan sanda sun nuna cewa dakarun tsaro sun ceto biyar daga cikinsu, ciki har da yaro mai shekara hudu.
Rundunar ta bayyana cewa a halin yanzu mutum tara na ci gaba da kasancewa a hannun wadanda ake zargi sun yi garkuwa da su.
Asali: Legit.ng

