Kwana Kadan bayan Tsira daga Hannun Yan Bindiga, Sarki a Arewa Ya Mutu
- Wani basarake a Kwara ya rasu kwanaki bayan kubutar da shi daga hannun masu garkuwa da mutane a Kwara
- An yi garkuwa da sarkin ranar 22 ga Agusta, kafin jami’an tsaro su kubutar da shi bayan kwana biyar yayin wani samame
- Dan sarkin ya tabbatar da rasuwarsa a asibiti bayan gajeriyar rashin lafiya, yayin da aka ce jami’an tsaro sun kubutar da mutane uku
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Igbesi, Kwara - Sarkin Igbesi, Oba Moses Oyinloye Iwedunmoye I, ya rasu kwanaki kadan bayan kubuta daga hannun yan bindiga.
Majiyoyi sun ce sarkin ya rasu bayan jami’an tsaro sun kubutar da shi daga hannun masu garkuwa a karamar hukumar Isin ta jihar Kwara.

Source: Original
Tun yaushe aka yi garkuwa da sarkin?
An yi garkuwa da sarkin ne ranar 22 ga Agusta, lokacin da wasu ‘yan bindiga dauke da makamai suka mamaye garin Igbesi, cewar Punch.
An sake shi bayan kwana biyar yayin wani samamen jami’an tsaro a yankin Elerin/Ijomu-Oro na jihar.
Shugaban kungiyar Omo Ibile Igbomina, Bisi Fakayode, ne ya sanar da rasuwar sarkin ranar Asabar, inda ya bayyana alhininsa tare da addu’ar Allah Ya jikansa.
Majiyoyi sun tabbatar da rasuwar ta hannun daya daga cikin ‘ya’yan sarkin, Prince Olasunkanmi, wanda ya ce mahaifinsa ya rasu a wani asibiti da sanyin safiyar Asabar.
Olasunkanmi ya ce:
“Eh, labarin gaskiya ne. Ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya da ta biyo bayan kubutar da shi. Mun kai shi asibiti ne da fatan zai tsira, amma ya rasu a can da sassafe.”
Sarkin na daga cikin mutane uku da jami’an tsaro suka kubutar yayin samamen da suka gudanar a yankin Elerin/Ijomu-Oro.

Source: Twitter
Yadda yan sanda suka kubutar da sarkin
Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta ce samamen ya biyo bayan samun bayanan sirri da suka kai ga ofishin ‘yan sandan Oro da misalin karfe 10 na safe.
Wani jami’in tsaron sa-kai ne ya kai rahoton cewa daya daga cikin mutanensa ya samu raunin harbin bindiga yayin da yake cikin daji a kusa da Elerin/Ijomu-Oro.
Daga nan ne jami’in ‘yan sandan yankin Oro ya jagoranci tawagar hadin gwiwa da ta kunshi ‘yan sanda, sojoji da jami’an tsaron sa-kai zuwa yankin.
A cewar ‘yan sanda, wadanda ake zargin masu garkuwa ne sun bude wuta bayan sun hango jami’an tsaron da ke tunkararsu, lamarin da ya haifar da musayar wuta.
A yayin musayar wutar, an kashe daya daga cikin wadanda ake zargin ‘yan garkuwa ne, yayin da sauran ‘yan kungiyar suka tsere zuwa cikin dajin da ke kewaye.
Jami’an tsaron sun bi sahun wadanda suka tsere, inda suka gano mutanen uku da aka yi garkuwa da su.
Daga bisani an kwashe wadanda aka kubutar zuwa wani asibiti domin ba su kulawar lafiya, cewar rahoton Vanguard.
Yan bindiga sun bankawa fadar Sarki wuta
Mun ba ku rahoton cewa 'yan bindiga kusan 200 sun kai wani mummunan hari a kauyen Woro dake jihar Kwara inda ake zargin sun hallaka fiye da mutane 35.
Maharan sun banka wa fadar Sarkin Woro wuta tare da shagunan dake kusa yayin da har yanzu ba a san inda sarkin ya shiga ba.
'Yan majalisar yankin sun bukaci gwamnatin tarayya ta tura dakarun soji na musamman domin kakkabe yan bindiga dake addabar Kaiama.
Asali: Legit.ng


