Babbar Dama: Gwamnatin Tarayya Za Ta 'Dauki' Yan Najeriya Miliyan 2 Aiki, An Ji Yadda Tsarin Yake

Babbar Dama: Gwamnatin Tarayya Za Ta 'Dauki' Yan Najeriya Miliyan 2 Aiki, An Ji Yadda Tsarin Yake

  • Gwamnatin Tarayya ta ce tana da burin samar da ayyukan yi miliyan biyu a masana’antar fasaha zuwa 2030
  • Hannatu Musawa ta bukaci masu fasaha a Arewa su mallaki ayyukansu tare da gina ingantattun tsarin kasuwanci
  • Ta ce Kano ta kasance tana da tattalin arzikin fasaha tun kafin a fara amfani da wannan kalma a manufofin tattalin arziki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirinta na samar da ayyukan yi ga mutne miliyan biyu a fannin fasaha zuwa shekarar 2030.

Gwamnatin ta ce tana ci gaba da kokarin ƙoƙarin mayar da al’adun ƙasar da baiwar masu fasaha zuwa harkokin kasuwanci masu samar da kuɗaɗen shiga.

Hanntu.
Ministar Fasaha, Al’adu, Yawon Buɗe Ido da Tattalin Arzikin Fasaha, Hannatu Musa Musawa Hoto: Hannatu Musa Musawa
Source: Facebook

Punch ta ruwaito cewa Ministar Fasaha, Al’adu, Yawon Buɗe Ido da Tattalin Arzikin Fasaha, Hannatu Musawa, ce ta bayyana hakan ranar Juma’a a wajen rufe taron Kano Creative Summit na 2026.

Kara karanta wannan

Houthi sun kwace yankin Bab al Mandab yayin da Saudi ke naman agajin Trump

Hannatu Musawa ta ƙalubalanci masu sana’ar fasaha a Arewacin Najeriya da su rike ayyukansu, su ƙarfafa tsarin kasuwancinsu, sannan su yi amfani da haƙƙin mallakar fasaha wajen samar da kuɗaɗen shiga masu ɗorewa.

Ayyukan fasaha sun dade a Kano

Ministar ta ce tsoffin al’adun fasaha na Kano sun nuna cewa birnin ya kasance yana da ingantaccen tattalin arzikin fasaha tun ƙarni da dama da suka gabata, tun kafin gwamnati ta shiga ciki.

Ta ambaci ramukan rini na Kano, sana’ar fata, saƙa, ɗinkin ado, ƙera ƙarafa, wasannin gargajiya da masana’antar fina-finai ta Kannywood a matsayin kadarorin fasaha da za su iya samar da gagarumar darajar tattalin arziki idan aka tsara su yadda ya kamata.

“Kano tana da tattalin arzikin fasaha tun kafin wani ya ba wa wannan masana’anta sunan tattalin arzikin fasaha,” in ji ta.

Ministar ta ce Kannywood ta samu dumbin masoya a ƙasashen duniya, inda fina-finanta ke isa ga al’ummomin masu magana da Hausa a faɗin Yammacin Afirka da kuma masu kallo a wasu sassan duniya.

Kara karanta wannan

Zance ya kare: Sanata Yari ya fadi abu 1 da za a tallata Tinubu da shi a Najeriya

Ta ce ya kamata a amince da gudummawar Kannywood a matsayin muhimmin ɓangare na masana’antar fina-finai ta duniya ta Najeriya tare da Nollywood.

Yadda ake samar da ayyukan yi

Ministar ta kuma jaddada gudummawar Kano wajen adabi, inda ta ce mata a birnin sun kasance suna rubuta, bugawa da sayar da littattafan labarai a kasuwannin cikin gida tun a shekarar 1958, kamar yadda Daily Post ta kawo.

Tinubu.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da ministar al'adu da fasahar kirkire-kirkire ta tarayya, Hannatu Musa Musawa Hoto: Hannatu Musa Musawa
Source: Getty Images

Ta kuma ce masu fasahar da ke da alaƙa da Zaria Art Society sun taka rawa wajen bunƙasa fasahar zamani a Najeriya.

“Gwamnatin Tarayya ta maida hankali kan shirye-shiryen tattalin arzikin fasaha, ciki har da tsari mai matakai takwas da manufar 2030, wanda ke da burin samar da ayyukan yi miliyan biyu a masana’antar fasaha zuwa 2030,” in ji ta.

An kawo shirin da zai taimaki yan Najeriya

Kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da shirin “Hire from Nigeria” domin hada kwararrun ’yan Najeriya da masu daukar ma’aikata na kasashen waje.

Gwamnatin ta kikiro shirin ne domin mayar da Najeriya cibiyar duniya wajen samar da kwararrun ma’aikata da ayyukan da ake yi ta hanyar fasahar zamani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262