Gwamnatin Tinubu Ta Raba Tallafin Naira Biliyan 600 ga Miliyoyin Yan Najeriya
- Gwamnatin Tarayya ta kashe sama da Naira biliyan 600 wajen tallafin kudi ga ’yan Najeriya masu rauni cikin shekaru uku
- Ministan Harkokin Jin Kai, Bernard Doro ya ce tallafin ya kai ga gidaje sama da miliyan 10 a wani mataki na rage wahalhalun rayuwa
- Ministan ya yi wannan bayani ne bayan da Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da shirin Renewed Hope Social Protection Programme na Dala biliyan daya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Gwamnatin Tarayya ta raba sama da Naira biliyan 600 a matsayin tallafin kudi ga ’yan Najeriya masu karamin karfi cikin shekaru uku da suka gabata.
Ministan Harkokin Jin Kai da Rage Talauci, Bernard Doro ne ya bayyana hakan, yana mai tabbatar da cewa miliyoyin talakawa sun amfana da wannan tallafi.

Source: Twitter
Doro ya bayyana hakan ne yayin wata hira da Channels Television a shirin Politics Today ranar Laraba, inda ya ce tallafin ya kai ga gidaje sama da miliyan 10.
“Mun bayar da sama da Naira biliyan 600 a matsayin tallafin kudi domin tallafa wa talakawa ’yan Najeriya cikin shekaru uku. Mun kai tallafin ga gidaje sama da miliyan 10,” in ji shi.
An kaddamar da shirin yakar talauci
Ministan ya yi wannan bayani ne bayan da Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da shirin Renewed Hope Social Protection Programme na Dala biliyan daya.
Shirin, an tsara shi ne domin taimaka wa ’yan Najeriya masu rauni su wuce matakin karbar tallafin wucin gadi zuwa dogaro da kai ta fuskar tattalin arziki.
Uwargidan Shugaban Kasa, Oluremi Tinubu, ce ta kaddamar da shirin, wanda ya kunshi Household Prosperity and Empowerment Social Protection Project (HOPE-SP).
Shirin na da nufin kafa tsarin tallafin jin kai na bai daya da zai mayar da hankali kan taimaka wa gidaje su fita daga kangin talauci.
Dalilin kirkiro shirin HOPE-SP
Doro ya ce sabon shirin zai bi wata hanya ta daban wajen rage talauci, inda gwamnati za ta rika bibiyar gidaje tare da auna ci gabansu wajen samun damar dogaro da kansu ta fuskar tattalin arziki.
“Mun samar da tsarin da za mu rika bibiyar halin da talakawa ke ciki,” in ji shi.
A cewarsa, shirin zai inganta hadin gwiwar ayyukan jin kai, tsarin tallafin al’umma da rage talauci, tare da sanya gidaje a matsayin cibiyar tallafin gwamnati.
Gidaje miliyan 7.6 za su amfana
Shirin HOPE-SP na da nufin tallafa wa gidajen talakawa kimanin miliyan 7.6 a fadin Najeriya.
Gidajen da suka cancanta za su samu tallafin kudi sau daya na N40,000 ta hanyar tsarin zamani na dijital domin taimaka musu fuskantar matsalolin tattalin arziki na gaggawa.

Source: Twitter
Masu cin gajiyar shirin dole ne su kasance cikin National Social Register, sannan a tabbatar da bayanansu ta amfani da katin dan kasa watau NIN.
Gwamnati na aiki tare da Hukumar Kula da Shaidar ’Yan Kasa ta Kasa (NIMC) domin saukaka rajistar NIN da kuma karfafa tsarin tantance wadanda suka cancanci tallafin.
Gwamnati ta fara shirin tallafawa matasa
Kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta sanar da wani sabon shiri da zai samar da tallafin kuɗi har Naira miliyan biyar ga zaɓaɓɓun matasa ’yan kasuwar Najeriya.
Shirin mai suna NiYA × Cascador Founders Programme, haɗin gwiwa ne tsakanin Nigerian Youth Academy ƙarƙashin Ma’aikatar Matasa da Ci Gaba.
Asali: Legit.ng

