Dama ga Matasa: An Kaddamar da Shirin da Yan Najeriya Za Su Samu Aiki a Kasashen Waje
- Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da shirin “Hire from Nigeria” domin hada kwararrun ’yan Najeriya da masu daukar ma’aikata na kasashen waje
- Gwamnati na son mayar da Najeriya cibiyar duniya wajen kwararrun ma’aikata da ayyukan da ake gudanarwa ta hanyar zamani
- Shirin na cikin matakan da gwamnati ke dauka domin samar da guraben ayyukan yi miliyan daya da ke da alaka da fitar da ayyuka zuwa kasashen waje
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da shirin “Hire from Nigeria” domin hada kwararrun ’yan Najeriya da masu daukar ma’aikata daga kasashen ketare.
Gwamnatin ta kikiro shirin ne domin mayar da Najeriya cibiyar duniya wajen samar da kwararrun ma’aikata da ayyukan da ake yi ta hanyar fasahar zamani.

Source: Twitter
An kaddamar da shirin samar da ayyuka

Kara karanta wannan
Lauya ya tsage gaskiya, an ji dalilin da ya sa Amurka ba ta kama Shugaba Tinubu ba
Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ne ya kaddamar da shirin a Abuja ranar Litinin, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Idris ya ce Najeriya na iya kara samun kudaden shiga daga kwarewa da ayyukan da ’yan kasar ke da su ba tare da bukatar su bar Najeriya su koma kasashen waje ba.
Ya ce tattalin arzikin duniya ya sauya yadda ilimi, kwarewa, kirkire-kirkire da ayyukan kwararru ke ketare iyakokin kasashe ta hanyar zamani ba tare da sun bar gidajensu ba.
Najeriya ta shirya fafatawa a duniya
Ministan ya kara da cewa yawan matasan Najeriya da kuma karuwar kwararrun ma’aikata ya sanya kasar cikin kyakkyawan matsayi na cin gajiyar wannan sauyi.
“Makomar tattalin arzikin Najeriya za ta kara dogaro ne kan hazaka, kirkire-kirkire, kwarewa da kwazon mutanenmu.
"Najeriya a shirye take ta fafata a fagen duniya. Kwararrun ’yan Najeriya a shirye suke su yi aiki. Kuma duniya ya kamata ta kalli Najeriya,” in ji ministan.
Idris ya kara da cewa shirin ya hada ma’aikatun masana’antu, kasuwanci da zuba jari; ilimi; da abokan hulda daga kamfanoni masu zaman kansu domin hada kwararrun ’yan Najeriya da bukatun kasuwannin duniya.
Yadda shirin gwamnati zai yi aiki
Ya kuma ce ma’aikatar yada labarai za ta yi amfani da kafafen sadarwarta da hadin gwiwa da abokan hulda wajen tallata kwararrun ’yan Najeriya da kamfanoninsu a kasashen duniya.

Source: Twitter
Ministan ya ce shirin ya yi daidai da ajandar Renewed Hope Agenda ta Shugaba Bola Tinubu da kuma burin gwamnati na samar da guraben ayyukan yi miliyan daya da ke da alaka da fitar da ayyuka zuwa kasashen waje.
“Matashin dan Najeriya ba dole ne ya bar kasar ba domin shiga harkokin tattalin arzikin duniya ba.
"Idan aka samu kwarewar da ta dace, ababen more rayuwa, ka’idojin aiki na kwararru da damar shiga kasuwanni, ’yan Najeriya za su iya rayuwa, su yi aiki kuma su samu kudaden shiga a nan gida,” in ji shi.
Gwamnatin Najeriya ta raba tallafin N600bn
Kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta raba sama da Naira biliyan 600 a matsayin tallafin kudi ga ’yan Najeriya masu karamin karfi cikin shekaru uku da suka gabata.
Ministan Harkokin Jin Kai da Rage Talauci, Bernard Doro ne ya bayyana hakan, yana mai tabbatar da cewa miliyoyin talakawa sun amfana da wannan tallafi.
Asali: Legit.ng
