Houthi Sun Kwace Yankin Bab al Mandab yayin da Saudi ke Naman Agajin Trump
- ’Yan Houthi sun bayyana cewa sun ƙwace iko da yankin Bab al-Mandab da tsibirin Mayyun bayan shafe mako guda suna kai hare-hare a Yemen
- Kwace yankunan na iya ƙara barazana ga zirga-zirgar jiragen ruwa a Bahar Maliya, tare da ƙara tsananta tasirin yaƙin Gabas ta Tsakiya ga harkokin kasuwancin duniya
- Farashin man fetur ya haura dala 100 kan kowace ganga a wannan makon, yayin da Amurka ta fuskanci tashin farashin dizal zuwa sama da dala 6 kan galan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Yemen – ’Yan Houthi a Yemen sun ƙara ƙarfafa matsayinsu a yankin Bab al-Mandab bayan wani samame da suka kwashe mako guda suna gudanarwa.

Source: Getty Images
Bab al-Mandab wata muhimmiyar mashiga ce ta kudancin Bahar Maliya da ke haɗa yankin da mashigin ruwa na Suez, hanyar da ake amfani da ita wajen jigilar kayayyaki tsakanin ƙasashe.

Kara karanta wannan
Kaico: An tsinci gawar budurwa a wani yanayi bayan ta yi faɗa da saurayinta a Kaduna
Houthi ta kwace Bab al-Mandeb
Rahoton ya zo ne sa’o’i kaɗan kafin AFP ta ruwaito cewa ’yan Houthi sun karɓe wani tsibiri da ke Bahar Maliya, wanda yake tsakiyar mashigar jiragen ruwa ta Bab al-Mandeb.
An ce sojojin gwamnatin Yemen sun janye daga tsibirin, lamarin da ya jawo kammala ƙoƙarin ’yan Houthi na ƙara faɗaɗa ikonsu a yankin.
’Yan Houthin da Iran ke mara wa baya sun kuma karɓe birnin Mocha, lamarin da ya ƙara masu tasiri a kan Bab al-Mandeb, ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin safarar kayayyaki ta ruwa a duniya.

Source: Getty Images
Amurka za ta taimaka wa Saudiyya
Wani babban jami’in gwamnatin Amurka ya ce Washington na mayar da hankali kan kare muhimman muradunta na tsaron ƙasa, ciki har da tabbatar da ’yancin zirga-zirgar jiragen ruwa a Bahar Maliya.
Ya ce Amurka na ci gaba da tattaunawa da Saudiyya da gwamnatin Yemen kan hanyoyin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Kara karanta wannan
Trump ya watsa wa Saudiyya kasa a ido, ya ki amince wa da rokon Yarima kan Houthi
Rahotanni sun ce akwai kusan sojojin Amurka 200 a Saudiyya da ke ba da tallafi, yayin da Admiral Brad Cooper, kwamandan Rundunar Sojin Amurka, ya garzaya Saudiyya ranar Alhamis.
Farashin mai ya haura dala 100
Farashin man fetur a kasuwannin duniya ya haura dala 100 kan kowace ganga a wannan makon, yayin da matsakaicin farashin dizal a Amurka ya haura dala 6 kan galan a karon farko ranar Juma’a.
France 24 ta wallafa cewa karin tashin farashin mai na iya ƙara matsin lamba kan gwamnatin Shugaba Donald Trump gabanin zaɓen Amurka.
Iran ta kai wa Amurka hari
A wani rahoton, kun ji cewa an bayyana cewa dakarun Iran sun kai hare-haren makamai masu linzami kan wuraren da ake ajiya da shirya jiragen yaƙin Amurka a Jordan.
Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran ta ce makamai masu linzamin sun lalata wuraren kula, shiryawa da tura jiragen F-35, F-16 da F-15, da kuma matsugunansu.
Rundunar Sojin Jordan ta ce an tare 18 daga cikin makamai masu linzami 20, yayin da biyu suka faɗi a wuraren da babu jama’a, kuma sojojin Amurka suka harba kusan makamai 30 na Patriot domin dakile harin.
Asali: Legit.ng