Mai Shekara 60 Ya Rasu bayan Zuwa Otel da Budurwa, an Samu Maganin Jima'i
- Rundunar 'yan sandan Jigawa ta fara bincike kan mutuwar wani mutum mai shekaru 60 da ya rasu bayan ya shiga otal tare da wata budurwa mai shekaru 20
- 'Yan sanda sun ce an gano abinci, abubuwan sha da kuma wani maganin ƙara ƙarfin jima'i da ake zargi a ɗakin da lamarin ya faru
- Kwamishinan 'yan sanda ya buƙaci jama'a su guji yaɗa jita-jita yayin da ake ci gaba da gudanar da cikakken bincike kan musabbabin mutuwar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Dutse – Rundunar 'Yan Sandan Jihar Jigawa ta fara gudanar da bincike kan mutuwar wani mutum mai shekaru 60 da ta faru a wani otal da ke birnin Dutse.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Lawan Shi'isu Adam, ya fitar a ranar Talata, ya ce lamarin ya faru ne a ranar 21 ga Yulin 2026.

Source: Original
Sanarwar SP Adam ya wallafa a Facebook ta bayyana cewa marigayin ya shiga otal ɗin tare da wata budurwa mai shekaru 20 kafin daga bisani ya samu matsalar lafiya ba zato ba tsammani.
Yadda tsohon ya mutu
A cewar rundunar, mutumin ya fara nuna alamun rashin lafiya ne bayan ya nemi a kawo masa abinci, inda aka ce ya fara fama da wahalar numfashi.
Bayan samun rahoton gaggawa, jami'an 'yan sanda daga sashen Yalwawa suka garzaya wurin tare da kai mutumin Babban Asibitin Dutse. Sai dai likitoci sun tabbatar da rasuwarsa bayan an duba lafiyarsa.
An samu maganin karfin maza
Bayan tabbatar da mutuwar mutumin, jami'an bincike sun killace wurin da lamarin ya faru domin gudanar da bincike.
Rundunar ta ce an gano wasu kayan abinci da abubuwan sha tare da wani abu da ake zargin maganin ƙara ƙarfin jima'i ne, da kuma wasu kayayyaki.
Sanarwar ta ce an bi dukkan matakan da suka dace wajen adana shaidu domin tabbatar da sahihancin binciken.
Bayan kammala binciken farko da tabbatar da mutuwar, an miƙa gawar mamacin ga iyalansa domin yi masa jana'iza bisa buƙatarsu.
Budurwar tana fitar da bayanai
Rundunar ta ce budurwar mai shekaru 20 da ke tare da mamacin a lokacin faruwar lamarin na ci gaba da ba masu bincike cikakken haɗin kai.
A cewar sanarwar, tana bayar da bayanan da za su taimaka wajen gano ainihin abin da ya jawo mutuwar mutumin.
Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Jigawa ya tabbatar da cewa za a gudanar da binciken cikin ƙwarewa, adalci da rashin son rai.

Source: Facebook
Ya kuma buƙaci mazauna jihar da su guji yaɗa jita-jita ko bayanan da ba a tabbatar da su ba, yana mai cewa za a sanar da jama'a duk wani sabon bayani idan binciken ya kai wani mataki.
Jigawa: An yi hadarin kwale-kwale
A wani labarin, mun ruwaito cewa mutum ɗaya ya mutu yayin da wasu 39 suka ɓace bayan wani kwale-kwale ɗauke da manoma da ma'aikatan gona ya kife a Jigawa.
Rundunar 'yan sandan jihar ta ce jami'anta tare da masu ceto da mazauna yankin sun fara aikin bincike da ceto bayan samun rahoton hatsarin.
Hukumomi sun ce har yanzu ba a gano musabbabin hatsarin ba, lamarin da ya sake jawo hankalin jama'a kan matsalolin sufurin ruwa a yankunan karkara.
Asali: Legit.ng

