"Ba Ruwan Tinubu," An Bayyana Wadanda Ake Turawa Kudin Tallafin Fetur da Aka Cire a Najeriya
- Gwamnan Ogun, Dapo Abiodun, ya ce gwamnoni ne ya kamata su yi bayanin yadda ake amfani da ƙarin kuɗin da aka samu bayan cire tallafin mai
- Abiodun ya ce cire tallafin ya ƙara yawan kuɗin da jihohi ke samu daga Asusun Tarayya na wata wata
- Gwamnan ya ce ana amfani da ƙarin kuɗin wajen gina ababen more rayuwa da sauran ayyukan ci gaba a jihohi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ogun, Nigeria - Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya ce ba Shugaba Bola Tinubu ya kamata yan Najeriya du tuhuma kan yadda aka yi da kudin tallafin mai da aka cire a Najeriya.
Gwamna Abiodun ya dora nauyin kan gwamnonin jihohi, yana mai cewa su ke ya kamata su yi wa mutane bayanin yadda kudin suka yi.

Source: Twitter
Ina kudin tallafin fetur suka yi?
A rahoton Daily Trust, Abiodun ya ce cire tallafin ya ƙara kuɗin da gwamnatocin jihohi ke samu, abin da ya sa gwamnonin suka fi dacewa su yi bayanin yadda ake amfani da ƙarin kuɗin.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani gangamin da Jam’iyyar APC mai mulki ta shirya a Ogun da nufin mayar da martani kan sukar da ’yan adawa ke yi game da yadda ake amfani da kuɗin da aka samu bayan cire tallafin fetur.
A cewar Abiodun, bai dace a nemi Tinubu ya yi bayanin abin da aka samu daga cire tallafin ba, alhali gwamnatocin jihohi na samun ƙarin kuɗi daga Asusun Tarayya.
Yadda gwamnoni ke kashe kudin tallafi
Ya ce gwamnonin na amfani da ƙarin kuɗin wajen gudanar da ayyukan more rayuwa da sauran ayyukan ci gaba a jihohinsu.
“Sun ce suna son a dawo da tallafin, ko dai sun haukace ne? Suna neman shugabanmu ya yi bayanin abin da ya yi da kuɗin da aka samu daga cire tallafin."

Kara karanta wannan
Shugaban Amurka ya 'tsorata', ya fara laluben lokacin dakatar da yaki da ƙasar musulunci ta Iran
“Mu ne ya kamata mu yi irin wannan bayanin, domin mu ne gwamnonin jihohi muke karɓar kuɗin daga tarayya.
“Bugu da ƙari, me muke amfani da shi wajen gina tituna, makarantu, samar da gidaje masu kyau da kuma tallafa wa manoma? Ashe ba daga kuɗin tallafin ba ne?”
- Gwamna Dapo Abiodun.

Source: Twitter
Kalaman gwamnan sun zo ne a daidai lokacin da ake sake yin muhawara kan tasirin cire tallafin man fetur ga tattalin arziki da kuma yadda aka raba tare da amfani da ƙarin kuɗin da gwamnati ta samu.
Abiodun ya kuma yi amfani da damar wajen sukar jam’iyyun adawa gabanin babban zaɓen 2027, yana mai nuna kwarin gwiwar cewa APC za ta doke abokan hamayyarta na siyasa, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Gwamna Abiodun ya gode wa Tinubu
A baya, kun ji cewa gwamnan Ogun, Dapo Abiodun , ya nuna godiya ga shugaban kasa, Bola Tinubu, bisa ziyarar da ya kai jihar dominnkaddamar da manyan ayyuka.
Abiodun ya bukaci shugaban kasar da ya ci gaba da yaki da aikata laifuffuka a kasar da kuma ta'addanci da ake fama da shi.
Asali: Legit.ng
