Melaye Ya Yi Gagarumin Gargadi da Tinubu idan EFCC Ta Kuskura Ta Cafke Atiku

Melaye Ya Yi Gagarumin Gargadi da Tinubu idan EFCC Ta Kuskura Ta Cafke Atiku

  • Dino Melaye ya gargadi gwamnatin tarayya kan gayyata ko cafke Atiku Abubakar inda ya yi barazanar daukar mataki
  • Melaye ya ce ADC za ta nuna cewa talakawan Najeriya sun fi wadanda ke cikin gwamnati yawa, tare da kare Atiku
  • Gargadin ya biyo bayan sabuwar kara da aka kai EFCC kan zargin almundahana da Atiku ya fuskanta lokacin suna mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon Sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya gargadi gwamnatin tarayya kan gayyata, cafke Atiku Abubakar.

Melaye ya ce ADC za ta tabbatar wa gwamnati cewa al’ummar Najeriya sun fi wadanda ke cikin gwamnati yawa, idan aka gayyaci Atiku ko aka cafke shi.

Dino Melaye ya gargadi Tinubu kan 'yunkurin' cafke Atiku
Sanata Dino Melaye da Bola Tinubu. Hoto: Dino Melaye, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Ya bayyana hakan ne a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Juma’a, yana mayar da martani kan wata kara da aka shigar gaban EFCC.

Kara karanta wannan

Sarkin ya ji dadin kokarin Uba Sani, ya fadi wahalar da sarakuna ke ciki

Dalilin Melaye na yin gargadi

Kalaman Melaye sun biyo bayan wata kara da tsohon dan Majalisar Wakilai, Ehiozuwa Agbonayinma, ya shigar gaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa, EFCC.

Agbonayinma ya bukaci hukumar ta sake bude binciken zarge-zargen cin hanci da aka taba yi wa Atiku tun lokacin da yake rike da mukamin mataimakin shugaban kasa.

Melaye ya ce:

“Wannan gargadinmu ne, idan saboda wadannan kararraki marasa tushe kuka gayyaci, kuka cafke ko kuka yi wa Atiku Abubakar tambayoyi, za mu tabbatar muku cewa wadanda ke cikin gwamnati ba su kai kashi daya cikin dari na al’ummar Tarayyar Najeriya ba. Za mu tabbatar muku cewa jama’a ne suka mallaki gwamnati.”

Lauyansa, Hannibal Uwaifo, SAN, ne ya sanya hannu kan takardar karar, wadda rahotanni suka ce ta yi ishara da wani tsohon bincike da rahoton EFCC kan zarge-zargen da suka shafi Atiku.

Kara karanta wannan

'Ni na ci zaɓe a 2023': Kalaman Obi da suka dugunzuma fadar shugaban ƙasa

Melaye ya yi gargadi kan zargin Atiku
Sanata Dino Melay, Atiku Abubaar da Bola Tinubu. Hoto: Dino Melaye, Asiwaju Bola Tinubu, Atiku Abubakar.
Source: Facebook

Tun yaushe ake zargin Atiku Abubakar?

Zarge-zargen sun samo asali ne daga shekarun 2005 da 2006, lokacin da EFCC da wata kwamitin gudanarwa suka binciki zargin amfani da mukami ba bisa ka’ida ba, safarar kudade da karkatar da wasu kudade.

An alakanta zargin da kudaden Asusun Raya Fasahar Man Fetur, wato Petroleum Technology Development Fund.

Atiku, wanda yake mataimakin shugaban kasa a lokacin, ya musanta aikata wani laifi, yana mai cewa zarge-zargen na da alaka da siyasa.

A ranar 20 ga Disamba, 2006, wata Babbar Kotun Jihar Lagos ta yi watsi da hukuncin gudanarwa na EFCC kan Atiku, inda ta bayyana shi a matsayin wanda ya saba wa kundin tsarin mulki kuma mai cike da kura-kurai.

Sabuwar karar ta zo ne a lokacin da Atiku ke shirin tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027 karkashin ADC, yayin da ‘yan adawa ke kokarin kalubalantar Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

'Abin da tsofaffin shugabanni ke tsoro Tinubu ya aiwatar saboda tausayin 'yan kasa'

Sanata Melaye, wanda ke cikin manyan masu goyon bayan Atiku da ADC, ya ce ‘yan adawa za su yi tir da duk wani yunkurin amfani da karar wajen kai wa tsohon mataimakin shugaban kasa hari.

Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, babu wata tabbatacciyar shaida da ke nuna cewa EFCC ta gayyaci ko ta cafke Atiku kan wannan sabuwar kara.

Ana zargin Dino Melaye bai biyan haraji

An ji cewa hukumomi na zargin cewa tsohon sanatan Kogi, Dino Melaye ya shafe shekaru biyu yana guje wa biyan harajin kudaden da ya samu.

Hukumar haraji ta Abuja (FCT-IRS) ta ce Dino Melaye ya ki biyan harajin fiye da Naira miliyan 509 na kudaden shigarsa.

Yanzu haka dai an gurfanar da Dino Melaye gaban kotu, kuma zai iya fuskantar hukuncin biyan harajin da wasu tara da za a ci shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.