Tura Ta Kai Bango: Mutane Sun Fusata kan Matsalar Rashin Tsaro a Sokoto
- Mazauna Tambuwal a jihar Sokoto sun fito kan tituna ranar Juma’a suna zanga-zangar nuna fushinsu kan yawaitar hare-hare da garkuwa da mutane
- Masu zanga-zangar sun buƙaci ƙarin jami’an tsaro da kayan aiki, tare da ƙarfafa sintiri da tattara bayanan sirri a yankunan da ke cikin haɗari
- Rundunar ’yan sandan Sokoto ta tabbatar da sanin lamarin, tana mai cewa jami’an tsaro suna daukar matakin da ya dace domin kare rayuka da dukiyoyi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Sokoto - Fushi da takaici sun mamaye ƙaramar hukumar Tambuwal ta jihar Sokoto, yayin da mazauna yankin suka fito kan tituna domin zanga-zangar nuna adawa da yawaitar hare-hare da garkuwa da mutane.
Mutanen da ke rayuwa a wajen sun ce tabarbarewar tsaro na ci gaba da yin barazana ga rayuka, sana’o’i da harkokin tattalin arziki a yankin.

Source: Original
Fargabar hare-hare ta jawo zanga-zangar
Jaridar Vanguard ta kawo rahoton cewa mutanen sun fito kan tituna ne a ranar Juma'a, 11 ga watan Satumban 2026.
Rahotanni sun ce zanga-zangar ta samu halartar mazauna wasu sassa na ƙaramar hukumar, sakamakon ƙara fargabar hare-hare da sace mutane da ake zargin miyagun ’yan bindiga da aikatawa.
Masu zanga-zangar sun bayyana matuƙar damuwa kan yadda rashin tsaro ke ci gaba da addabar yankin.
Sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jihar Sokoto da su ɗauki matakan gaggawa da tsauri domin kare al’umma daga ƙarin hare-hare.
Manoma da ’yan kasuwa na cikin fargaba
Masu zanga-zangar sun koka da cewa hare-haren da ake ci gaba da samu sun haifar da yanayin tsoro, musamman tsakanin manoma, ’yan kasuwa da mazauna karkara.
Sun ce rayuwar waɗannan mutane ta dogara ne kan samun damar zuwa gonaki, kasuwanni da sauran wuraren gudanar da harkokin tattalin arziki cikin ’yanci.
Sun kuma yi gargaɗin cewa ci gaba da rashin tsaro na iya kawo cikas ga noman abinci tare da tilasta wa mazauna barin gidajensu da gonakinsu zuwa wuraren da suka fi aminci.
Sun nemi ƙarin jami’an tsaro
Masu zanga-zangar sun buƙaci a tura ƙarin jami’an tsaro da kayan aiki zuwa al’ummomin da ake ganin suna cikin haɗari.
Sun ce ya kamata hukumomin tsaro su ƙara sintiri, sa ido da kuma amfani da bayanan sirri domin gano tare da dakile hare-haren kafin su faru.
Haka kuma, sun yi kira da a ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin sojoji, ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro domin bin sawun masu aikata laifukan da kuma dawo da amincewar jama’a.
’Yan sanda sun ce suna kokari
Da yake mayar da martani kan damuwar da ake nunawa, Rundunar ’Yan Sandan Jihar Sokoto ta tabbatar da cewa tana sane da halin da ake ciki.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Ahmad Rufai, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce ’yan sanda na sanya ido kan yankin tare da ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyi.

Kara karanta wannan
Dan takara ya yi alkawarin samar da lantarki a kowane gida cikin watanni 11 a Najeriya

Source: Facebook
'Yan bindiga sun kashe mutane a Sokoto
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga da ake zargin yaran Bello Turji ne, sun hallaka akalla mutane 10 a Sokoto.
Maharan sun kuma yi awon gaba da mutane 40 zuwa cikin daji bayan sun kwashe kusan sa'o'i suna cin karensu babu babbaka.
Asali: Legit.ng

