Kwankwaso Ya Dauki Zafi kan Kisan Dan Shagamu, Ya Sha Babban Alwashi

Kwankwaso Ya Dauki Zafi kan Kisan Dan Shagamu, Ya Sha Babban Alwashi

  • Madugun Kwankwasiyya ya bayyana damuwa kan kisan shahararren mai sharhin siyasa a kafafen sada zumunta, Ibrahim Khalil Dan Shagamu, a Kano
  • Ya buƙaci Gwamnatin Kano ta kafa kwamitin bincike domin gano waɗanda suka aikata kisan tare da gurfanar da su a gaban shari’a
  • Rabiu Musa Kwankwaso ya yi kira ga Gwamnatocin Jiha da Tarayya su kare masu sukar gwamnati, yana mai cewa kundin tsarin mulki ya ba kowa ’yancin faɗar albarkacin baki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana matuƙar damuwarsa kan kisan shahararren mai sharhin siyasa a kafafen sada zumunta, Ibrahim Khalil Dan Shagamu.

Marigayi Ibrahim Khalil Dan Shagamu ya rasu ne bayan da aka tsinci gawarsa cikin jini a gidansa da ke Kano.

Kwankwaso ya yi Allah wadai da kisan Dan Shagamu
Marigayi Ibrahim Khalil Dan Shagamu da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: @KwankwasoRM
Source: Twitter

Madugun na Kwankwasiyya ya yi magana kan kisan da aka yi wa Dan Shagamu ne a wani rubuti da ya yi a shafinsa na X ranar Laraba, 9 ga watan Satumban 2026.

Kara karanta wannan

Magana ta girma: Amnesty ta shiga lamarin kisan Ɗan Shagamu a Kano

Ya ce Dan Shagamu ya mutu ne sakamakon mummunan hari, inda ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta gaggauta kafa kwamitin bincike domin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

An bukaci a kamo waɗanda suka yi kisan

Kwankwaso ya buƙaci hukumomin Kano su gudanar da bincike cikin tsanaki domin gano waɗanda suka aikata kisan tare da gurfanar da su a gaban kotu.

Ya ce idan hukumomi suka gaza ɗaukar matakin da ya dace cikin gaskiya da kuma bayyana abin da aka gano, gwamnatin NDC mai zuwa za ta gudanar da cikakken bincike bayan ta karɓi mulki.

Ya kuma ce za a ɗauki dukkan matakan da suka dace domin tabbatar da cewa waɗanda ke da hannu a kisan sun fuskanci hukunci.

Ya nemi a kare masu adawa da gwamnati

Kwankwaso ya kuma yi kira ga Gwamnatocin Jihar Kano da Tarayya da su tabbatar da kariyar masu bayyana ra’ayoyin adawa daga duk wani hari ko barazana.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya yi magana mai tsauri kan kisan fitaccen mai sharhi kan siyasa a Kano

A cewarsa, Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya bai wa dukkan ’yan ƙasa ’yancin faɗar albarkacin baki.

Ya ce wannan haƙƙi ya kamata ya kare kowa daga barazana, hari da kuma tsoratarwa saboda ra’ayinsa na siyasa.

Kwankwaso ya yi ta’aziyya ga iyalan Dan Shagamu

Kwankwaso ya buƙaci hukumomin Najeriya su tabbatar da gudanar da cikakken bincike kan kisan tare da hukunta duk waɗanda aka samu da hannu a lamarin.

Ya kuma miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan Ibrahim Khalil Dan Shagamu, abokansa da kuma mabiyansa.

“Allah Maɗaukaki Ya gafarta masa, Ya kuma ba shi Jannatul Firdaus. Amin,” in ji Kwankwaso.
Kwankwaso ya yi magana kan kisan Dan Shagamu
Madugun Kwankwasiyya na gabatar da jawabi Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

An cafke mutum biyu kan kisan Dan Shagamu

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Kano ta sanar da kama mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan Ibrahim Khalil Dan Shagamu.

Rundunar ta bayyana cewa miyagun ne suka kutsa gidan mamacin da karfi,.sannan kuma suka masa da rauni da abubuwa masu kaifi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng