Karin Kudin Fetur babu Makawa yayin da Ake Wayyo Lita Ta Haura N1300
- Farashin danyen mai na Brent ya koma sama da $107 rikicin Houthi da Saudi da matsalar wucewa ta Hormuz
- Tsadar man fetur zai iya tsananta a Najeriya domin yanzu haka lita ta wuce N1,400 a sassa da dama na kasar
- Masana harkokin tattalin arziki sun gargadi cewa rikicin gabas ta tsakiya zai iya kara harba kudin gangar mai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
US - Danyen mai yana ta kara tsada a kasuwar duniya a sakamakon tashin hankalin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya.
Maganar da ake yi, gangar danyen mai yanzu ta haura $100 saboda dar-dar da aka shiga, ana tunani kaya za su yanke.

Source: Getty Images
Rigimar Houthi da Saudi ya tashi kudin mai
Rahoto daga tashar CNN ya ce farashin gangar man Brent ya karu da sama da 3.3% a ranar Laraba, ya haura $100 yanzu.
Wannan ne karon farko da gangar Brent ya wuce $100 tun bayan watan Yuli kuma mafi girman tashinsa cikin tsawon watanni.
Shi ma danyen man Amurka ya tashi da 3.25%, duk ma’ana ganga daya ta zarce $96 a kauwa.
An samu wannan tashin farashi ne a lokacin da rikicin kasar Saudi Arabiya da ‘yan Houthi yake kara muni a gabas ta tsakiya.
Ganin haka ne ake tunani babu abin da zai hana a ga canjin kudin litan fetur a gidajen mai tunda kasuwar duniya ta tabu.
Fetur ya tashi daga N800 zuwa N1300
Sanadiyyar rikicin kasar Iran da Amurka sai da fetur ya tashi a Najeriya tun daga N800 har zuwa sama da N1, 300 a halin yanzu.
A farkon shekara kafin a fara rikicin Iran da Amurka, ganga tana kasa da $70 ne, wannan ya sa fetur yake a rabin farashinsa na yau.
Danyen mai yana ta kara kudi a duniya
Sababbin bayanan da ake samu daga shafin Oilprice.com sun ce danyen man Najeriya ma ya kai $107 zuwa yammacin Alhamis.
Toshe hanya da aka yi a mashigar Hormuz ya taka rawar gani wajen tsadar ganga tunda jirage suna shan wahalar jigilar kayayyaki.
Kudin gangar West Texas Intermediate shi ma ya wuce $100 yanzu da ake fama da karancin mai da yake shiga kasashe a duniya.
Man fetur zai sauko a Najeriya?
This Day ta ce masana suna ganin za a yi ta fama da tsadar saboda babu abin da yake nuna Amurka da Iran za su sasanta nan kusa.
Dole ‘yan kasuwan duniya suka sake lissafi wanda a karshe za a ji tasirin shi a Najeriya duk da kasar tana da matatun tace mai.
An dogara sosai da Aliko Dangote, sai dai shi ma matatarsa ta kan samu danyen mai har daga kasashen duniya masu arziki.
Baya ga haka, har gobe akwai ‘yan kasuwan da yawa da suke shiga kasashen waje domin su shigo da man da za su saida a gida.

Source: Getty Images
'Yan takaran ADC na goyon bayan tallafin fetur
Legit ta rahoto gwamnatocin ADC a Arewa maso yamma za su goyi bayan rage kudin fetur, karin albashi da samar da tsaro a yankin.
Masu neman zama gwamnonin sun rattaba hannu kan yarjejeniyar maido da tallafin man fetur don saukaka wa al'umma nauyin rayuwa.
Kai albashi fiye da N100, 000 yana cikin alkawuran da ‘yan takaran ADC masu neman gwamna Arewa maso yamma suka dauka.
Asali: Legit.ng


