Zanga Zanga Ta Barke a Sokoto kan Tsare Malamin Addinin Musulunci

Zanga Zanga Ta Barke a Sokoto kan Tsare Malamin Addinin Musulunci

  • Matasa sun toshe wasu hanyoyi tare da gudanar da zanga-zanga a Sokoto, suna neman a saki malamin addini Dahiru Mai Barewa da ke tsare bisa umarnin kotu
  • An samu arangama tsakanin masu zanga-zangar da jami’an tsaro bayan wasu matasa sun yi ƙoƙarin kwace malamin daga hannun jami’an da ke tsare da shi
  • Mai Barewa na fuskantar zarge-zargen barazanar kisa ga Sheikh Musa Ayyuba Lukuwa da Malam Murtala Bello Assada a wasu bidiyoyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Sokoto - An ɗan samu tashin hankali a wasu sassan birnin Sokoto bayan wasu matasa sun gudanar da zanga-zangar adawa da ci gaba da tsare malamin addini, Dahiru Mai Barewa.

Masu zanga-zangar sun bukaci a saki Mai Barewa, inda suka toshe wasu hanyoyi tare da gudanar da zanga-zanga a sassa daban-daban na birnin.

Kara karanta wannan

An rage mugun iri a Arewa, hatsabibin dan bindiga ya bakunci lahira a Zamfara

Matasa sun yi zanga-zanga a Sokoto
Taswirar jihar Sokoto, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar The Punch ta kawo rahoton cewa matasan sun gudanar da zanga-zangar ne a ranar Litinin, 7 ga watan Satumban 2026.

Sai dai jami’an tsaro sun shiga lamarin domin dawo da zaman lafiya da kuma hana lamarin ƙara ta'azzara.

Dalilin gudanar da zanga-zangar

Zanga-zangar ta biyo bayan umarnin kotu da ya bayar da umarnin sake kama Mai Barewa tare da ci gaba da tsare shi.

Malamin na fuskantar zarge-zargen yin barazanar kisa ga malaman addinin Musulunci, Sheikh Musa Ayyuba Lukuwa da Malam Murtala Bello Assada.

Lamarin ya jawo hankalin jama'a a Sokoto saboda alaƙarsa da addini, musamman ganin irin goyon bayan da Mai Barewa ke samu daga wasu matasa da kuma al’umma.

Matasan da suka gudanar da zanga-zangar sun nuna adawa da hukuncin kotun, suna cewa ya kamata a bi tsarin doka wajen magance matsalar. Sun kuma bukaci abin da suka kira “adalci da mutunta bin doka.”

An samu arangama da jami’an tsaro

Kara karanta wannan

Yadda aka jefar da jarirai a kango cikin ban tausayi bayan an haife su a Abuja

Sai dai lamarin ya ƙara yin zafi bayan wasu daga cikin masu zanga-zangar sun kai hari kan jami’an tsaro, yayin da suke ƙoƙarin ganin an saki Mai Barewa da ƙarfi.

Wata majiya da ta san abin da ya faru ta ce masu zanga-zangar sun yi ƙoƙarin ɗaukar doka a hannunsu domin kuɓutar da malamin.

“Sun yi ƙoƙarin ɗaukar doka a hannunsu tare da kuɓutar da shi da ƙarfi daga hannun jami’an da ke tsare da shi,” in ji majiyar.

Daga bisani, jami’an tsaro sun ƙara yawan jami’ansu a wuraren domin shawo kan lamarin da kuma hana ci gaba da rikici.

Arangamar ta haifar da tsaiko na ɗan lokaci ga zirga-zirgar ababen hawa a wasu wuraren da abin ya shafa.

Zarge-zargen barazana kan Mai Barewa

Shari’ar Mai Barewa ta samo asali ne daga wasu jerin bidiyoyi da ake zargin an gan shi yana yin barazana ga Sheikh Lukuwa da Malam Assada.

Rahotanni sun ce bidiyon ya haifar da damuwa tsakanin mazauna yankin, lamarin da ya sa aka fara kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da bincike.

A cewar rahotanni, Mai Barewa ya danganta zargin barazanar da ya yi wa Sheikh Lukuwa da wasu kalaman da aka danganta wa malamin game da iyayen Annabi Muhammad (SAW). A wani bidiyo kuma, an ce ya yi magana kan rashin jituwarsa da wasu hukumomi.

Kara karanta wannan

An kama dalolin bogi na Naira miliyan 30 ana kokarin shiga da su jama'a

An yi zanga-zanga a Sokoto
Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto Hoto: Jibwis Hq Jos
Source: Facebook

Masu zanga-zanga sun toshe titi a Abuja

A wani labarin kuma, kun ji cewaatasa sun mamaye tituna a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja, yayin da zanga-zanga kan matsalar rashin tsaro.

Masu zanga-zangar suka toshe wata gada da ke kan babban titin Karu-Nyanya, lamarin da ya haifar da cunkoson ababen hawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng