Ana Zargin Bello Turji da Kai Mummunan Hari a Sokoto da Aka Sace Mutane 40

Ana Zargin Bello Turji da Kai Mummunan Hari a Sokoto da Aka Sace Mutane 40

  • Akalla mutane 10 ne suka mutu, yayin da aka sace wasu 40 bayan ’yan bindiga da ake zargin mabiyan Bello Turji sun kai hari Tofa
  • Wani mazaunin Tofa ya ce maharan sun bude wa jama’a wuta, suka yi garkuwa da mutane tare da sace dabbobi kafin komawa daji
  • ’Yan Tofa da kauyukan da ke makwabtaka da su sun bukaci gwamnati da jami’an tsaro su kara yawan sojoji domin hana sake kai hare-hare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Sokoto - Akalla mutane 10 ne aka kashe, yayin da wasu 40 suka shiga hannun masu garkuwa da mutane bayan wasu ’yan bindiga da ake zargin mabiyan Bello Turji ne sun kai hari.

Rahotanni sun ce harin ya fara ne da misalin karfe 1 na dare, kuma ya dauki kusan sa’o’i hudu kafin maharan su janye.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun bindige babban manajan banki a Najeriya har ya mutu

Ana zargin yaran Bello Turji sun kai hari a Sokoto da aka kashe mutane 10
Taswirar jihar Sokoto da ke fama da matsalar tsaro. Hoto: Legit.
Source: Original

Wannan hari shi ne na baya-bayan nan cikin jerin hare-haren tashin hankali da ke addabar al’ummomin yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, cewar Leadership.

Abin da mazauna yankin ke cewa

Wani mazaunin garin, Ibrahim Sidi, ya ce maharan, wadanda ake zargin ’yan ta’adda ne da ke karkashin tasirin Bello Turji, sun mamaye Tofa tare da bude wa jama’a wuta.

Ya ce ’yan bindigar sun yi garkuwa da mutane da dama, sannan suka yi awon gaba da dimbin dabbobi kafin su koma cikin daji.

Sai dai Sidi ya bukaci sojoji kada su sassauta kokarinsu na bin diddigin tare da kama manyan shugabannin ’yan ta’adda, ciki har da Turji.

Wani mazaunin garin, Umar Kebbe, ya tabbatar da adadin wadanda aka kashe, inda ya kara da cewa maharan sun kuma kwashe kayayyaki tare da awon gaba da shanu da dama.

Kebbe ya zargi Bello Turji, wani fitaccen shugaban ’yan bindiga da ake zaton yana aiki daga makwabciyar Zamfara, da kitsa harin, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Jirgin sojoji ya saki bama bamai a Zamfara, an kashe Kachalla Gurgu

“Turji ba ya sama da doka. Dole a dauki mataki a kansa."

- in ji shi

Karamar hukumar Rabah tana iyaka da Zamfara, wadda ta dade tana fama da matsalar satar mutane, ’yan bindiga da kuma kungiyoyin masu satar shanu.

Mohammed Nahuche, wanda ya yi magana da LEADERSHIP, ya bayyana wasu daga cikin wadanda aka kashe a harin.

Ya ce wadanda aka kashe sun hada da Malam Muhammadu, Danbakanike, Musa Dan Agaji, Masaudu Basiru, Buba Biti, Yar Kuluwa Basiru da Jamila Umma.

An sace mutane 40 a Sokoto
Gwamna Ahmad Aliyu na jihar Sokoto. Hoto: Sokoto State Government.
Source: Twitter

Daga cikin wadanda aka sace

Daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su akwai Shafiu Bello, Bilyaminu Abubakar, Saifullahi Buhari, Hauwau Zayyanu da Saratu Ibrahim.

Sauran sun hada da Safiyya Nasi, Zulaiha Aminu, Bilya Abu, Farida Lawali, Yar Kadan Aminu da Kulu Amadu.

Nahuche ya kara da cewa daga bisani ’yan bindigar sun saki mutane 10 daga cikin wadanda suka yi garkuwa da su, yayin da suke tafiya da sauran wadanda aka kama zuwa maboyarsu.

Haka kuma, an samu rahoton wasu karin mutane biyu da aka yi garkuwa da su a kauyen Saburu da ke kusa, ciki har da wani manomi mai suna Sani Gayya.

Kara karanta wannan

Jamhuriyar Nijar ta faɗi ƙasashen da take zargi da yunkurin yi mata juyin mulki

Mazauna Tofa da sauran al’ummomin da ke makwabtaka da yankin yanzu haka suna kira ga gwamnatin tarayya da jami’an tsaro su tura karin dakaru Rabah.

Sun ce hakan zai taimaka wajen dakile karin hare-hare a Rabah da sauran al’ummomin da ke kan iyakar Sokoto da Zamfara.

An yi zanga-zanga a Sokoto kan tsare malami

Mun ba ku labarin cewa Matasa sun toshe wasu hanyoyi tare da gudanar da zanga-zanga a Sokoto, suna neman a saki malamin addini.

Dahiru Mai Barewa da ke tsare bisa umarnin kotu An samu arangama tsakanin masu zanga-zangar da jami’an tsaro bayan wasu matasa sun yi ƙoƙarin kwace malamin daga hannun jami’an da ke tsare da shi.

Mai Barewa na fuskantar zarge-zargen barazanar kisa ga Sheikh Musa Ayyuba Lukuwa da Malam Murtala Bello Assada a wasu bidiyoyi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.