Magana Ta Girma: Amnesty Ta Shiga Lamarin Kisan Ɗan Shagamu a Kano

Magana Ta Girma: Amnesty Ta Shiga Lamarin Kisan Ɗan Shagamu a Kano

  • Amnesty International ta yi Allah-wadai da kisan wani mai sharhi kan siyasa a kafafen sada zumunta, Ibrahim Khalil Dan Shagamu, a Kano
  • Kungiyar ta bukaci hukumomin Najeriya su gudanar da cikakken bincike tare da gurfanar da duk wadanda ake zargi da hannu a kisan nasa
  • Amnesty ta ce tana damuwa da barazana da tsoratar da masu ra’ayin siyasa yayin da zaben ke kara gabatowa a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Kisan Ibrahim Khalil Dan Shagamu a jihar Kano ya jawo maganganu daga bangarori da dama na Najeriya

Amnesty International ta yi Allah-wadai da kisan wani mai sharhi kan siyasa a kafafen sada zumunta wanda aka gano gawarsa cikin jini a gidansa da ke Gaida, Kano.

Kara karanta wannan

'Yan uwan Dan Shagamu da aka kashe a Kano sun bayyana wani sirri kafin mutuwarsa

Amnesty ta bukaci binciken kisan Dan Shagamu
Marigayi Ibrahim Khalil da aka kashe a Kano da wasu da ake zargin suna da hannu. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa.
Source: Facebook

Amnesty ta bayyana haka ne a cikin wani rubutu da ta yi a shafin X a jiya Laraba 9 ga watan Satumbar shekarar 2026.

Yadda aka kashe Dan Shagamu a Kano

Legit Hausa ta ruwaito cewa an yi wa Dan Shagamu kisan gilla bayan wadanda suka kashe shi sun rinjaye shi.

An kashe fitaccen mai sharhi kan harkokin siyasa na jihar Kano, Ibrahim Khalil Dan Shagamu, a gidansa.

Yan uwansa sun ce wasu mutane da har yanzu ba a gano su ba sun kai wa marigayin hari bayan sun kutsa gidansa, inda suka yanka shi har lahira.

Bukatar Amnesty ga hukumomi a Kano

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International Nigeria ta yi kira ga rundunar yan sanda da ta gudanar da bincike tare da hukunta makasan.

Amnesty ta bukaci jukumomin Najeriya su gudanar da bincike tare da tabbatar da an hukunta masu hannu.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya yi magana mai tsauri kan kisan fitaccen mai sharhi kan siyasa a Kano

Ta ce a tsarin dimokuradiyya, ana bai wa masu bayyana ra’ayinsu da masu sukar gwamnati damar magana, a saurare su, ba a kashe su ba saboda ra’ayinsu.

Amnesty ta nuna matukar damuwa cewa gwamnatin Najeriya ba ta yin isasshen kokari wajen dakile kashe-kashe, barazana, tsoratarwa da sauran munanan take hakkin dan Adam.

Yayin da zabuka ke gabatowa, Amnesty ta ce tana ci gaba da samun rahotanni masu tayar da hankali kan barazanar kisa da tsoratarwa da suka shafi siyasa.

Ta ce:

"Dole ne hukumomin Najeriya su gudanar da bincike kan wannan lamari tare da tabbatar da cewa an gurfanar da wadanda ake zargi da hannu a gaban kotu domin a hukunta su.
Yayin da zaɓe ke ƙaratowa, muna ci gaba da samun rahotanni masu tayar da hankali na barazanar kisar mutane da tsoratarwa da suka shafi siyasa."

Dan Shagamu: An kama wasu da ake zargi

Mun ba ku labarin cewa yan sandan jihar Kano sun sami nasarar cafke mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan wani mutum a yankin Gaida.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya dauki zafi kan kisan Dan Shagamu, ya sha babban alwashi

Rahoto ya ce maharan sun kutsa cikin gidan mamacin ne a daren Litinin inda suka farmake shi da makamai masu kaifi wanda ya yi sanadiyar mutuwarsa.

Kwamishinan yan sandan jihar ya mika sakon ta'aziya ga iyalan mamacin tare da tabbatar da gudanar da bincike mai zurfi domin tabbatar da an gurfanar da su a gaban kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.